Rufe samaniyar Nijar ya ƙara tsawon tafiyar jiragen Faransa a Afirka

An wallafa

Shugabannin da suka yi juyin mulki a Nijar sun rufe sararin samaniyar ƙasar har zuwa wani lokaci a nan gaba, inda suka kafa hujja da barazanar ɗaukar matakin sojoji daga ƙasashe maƙwabtansu.

Lamarin ya zo ne bayan ƙungiyar Ecowas ta nemi a sake mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki a ranar Lahadi.

Babu wata alama ta ɗaukar wani matakin sojoji, yayin da ƙungiyar Ecowas ta sanya ranar Alhamis don gudanar da wani taro bayan ƙarewar wa'adin da ta bai wa Nijar.

Faransa ta gargaɗi ‘yan ƙasarta a kan su guji yin duk wata tafiya zuwa Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, ƙasashen da suka nuna goyon baya ga sojoji masu juyin mulki.

Kamfanin sufurin jirgin saman Faransa na Air France ya dakatar da dukkan tafiye-tafiye.

Bayanai sun ce ƙarin jiragen sama na ƙasashen Turai sun ba da rahoton fuskantar katsewar sufuri har ma sun dakatar da jigila a faɗin nahiyar bayan rufe sararin samaniyar na Nijar a ranar Lahadi.

Cibiyar bin diddigin hada-hadar jiragen sama ta FlightRadar24, ta wallafa cewa rufe sararin samaniyar Nijar ya yi gagarumin ƙara faɗin yankin da mafi yawan jiragen fasinja ba za su iya wucewa ta ciki ba, a kan hanyarsu ta zuwa Kudancin Afirka daga Turai.

Matakin na hukumomin Nijar ya ƙara a kan ƙasashe irinsu Libya da Sudan da suka rufe sararin samaniyarsu a Afirka, inda wasu tafiye-tafiyen za su iya fuskantar ƙarin nisan kilomita 1,000 a zagayen da jiragen sama za su yi.

Wani mai magana da yawun kamfanin Air France ya ce jiragen saman kamfanin na sa ran ƙara tsawon lokacin tafiya daga filayen jiragen sama na ƙasashen kudu da hamadar Sahara, yayin da sufuri tsakanin filin jirgin saman Charles de Gaulle a Paris zuwa Accra zai kasance kai tsaye babu cin zango.

Tuni kamfanin sufurin jirgin saman Faransa na Air France ya dakatar da jigila zuwa birnin Ouagadougou na Burkina Faso da kuma Bamako na ƙasar Mali har zuwa 11 ga watan Agusta.

Matakin da ya rage wa Ecowas bayan Nijar ta yi biris

Sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar na jiran martanin da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) za ta ɗauka bayan cikar wa'adin da ta ba su na mayar da hamɓararren shugaban ƙasar a kan mulkin.

Ecowas ta ce rashin mayar da Bazoum kan karagar mulki na iya janyo ɗaukar "duk wani mataki".... ciki har da amfani da ƙarfin sojoji.

Ƙungiyar ta taɓa tura sojoji zuwa wasu ƙasashen yankin lokacin da suka yi fama da tarzoma a baya.

Nijar dai ta ce ta rufe sararin samaniyarta ba shiga ba fita ta sama.

Ƙungiyar ƙasashen ta ɗauki wannan tsattsauran mataki ne a kan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga watan Yuli, fiye da yadda aka saba gani baya.

Juyin mulkin Nijar shi ne na bakwai a cikin shekara uku.

Ƙimarta tana cikin hatsari saboda ta ce ba za ta lamunci wani ƙarin juyin mulki ba.

A Najeriya, maƙwabciyar Nijar, ɓangarori da dama na ta kiraye-kiraye ga hukumomi da ma Ecowas a kan su kauce wa ɗaukar matakin da zai tsunduma yankin Afirka ta Yamma cikin wani yaƙin.

Ƙasashen Italiya da Jamus a ranar Litinin sun yi kira ga Ecowas ta ƙara wa'adin da ta bai wa sojoji masu mulkin Nijar don ganin sun mayar da Shugaba Mohamed Bazoum a kan mulki bayan an zaɓe shi bisa tsarin dimokraɗiyya ko kuma su fuskanci matakin soji.

Sai dai Birtaniya ta “dage” a kan cewa “sai an kawo ƙarshen sace wa mutane ‘yancinsu na dimokraɗiyya a Nijar", cewar ministan harkokin Afirka.

Da yake zantawa da BBC, Andrew Mitchell ya ce "ba zai yiwu kawai wasu mutane da bindigogi su zo su ƙwace ragamar wata ƙasa ta irin wannan hanya ba kamar yadda muka gani a Nijar, saboda haka ne yake da muhimmanci a kai su ƙasa.”

"Duk abin da za a yi, sai an yi domin rusa juyin mulki da mayar da ‘yancin dimokraɗiyya hannun jama’ar Nijar, kuma a kan haka muka dakatar da agajin raya ƙasa da muke bayarwa, kamar yadda Asusun ba da Lamuni na Duniya da Bankin Duniya har ma da sauran ƙasashe suka yi".

Ministan harkokin wajen Italiya ya faɗa wa jaridar La Stampa cewa "Hanya ɗaya kawai, ita ce ta diflomasiyya".

"Ina fatan cewa wa'adin da ƙungiyar raya arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma wanda ya ƙare cikin tsakar dare, za a ƙara tsawaita shi a yau," in ji shi.

"Jazaman ne a samo mafita, don kuwa ba haa ba ne a ce babu wata hanya da za a iya bi sai ta yaƙi."

Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta nanata kiraye-kirayen lalubo mafita ta hanyar diflomasiyya maimakon yaƙi.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar ya ce Jamus tana goyon bayan Ecowas a ƙoƙarinta na shiga tsakani da take ci gaba da yi.

Ƙungiyar Ecowas dai ta yi Allah-wadai da juyin mulki bakwai da aka samu a yankin Afirka ta Yamma a cikin shekara uku.

Nijar mai albarkatun yureniyam da man fetur, na fama da hare-hare daga masu iƙirarin jihadi, tana kuma da muhimmanci ga ƙasashen Amurka da Turai da China da kuma Rasha.

Sojojin Nijar dai tuni suka sanar da rufe sararin samaniyar ƙasar, har sai abin da hali ya yi, abin da ke ƙara nuna fargabar da ake da ita ta yiwuwar amfani da ƙarfin soji.

Wasu dai na tsoron cewa shiga takun-saƙa da Ecowas, zai ƙara hargitsa yankin da ke fama da talauci da matslar ƙarancin abinci da hare-haren mayaƙa, abin da ke janyo mutuwar dubban mutane da tilastawa miliyoyi tserewa.

Manyan hafsoshin tsaro na ƙasashen Ecowas tuni suka ce sun amince da wani shiri na amfani da ƙarfin soja, wanda ya ƙunshi tantance wuraren da za su kai wa hari, muddin ba a mayar da shugaba Mohamed Bazoum da aka hamɓarar kan mulki ba.

A ranar Lahadi, ƙasar Italiya ta sanar da rage yawan dakarunta a Nijar domin bai wa ƴan ƙasar mafaka a sansanin sojinta idan al'amura suka rincaɓe.

Ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya ce "kamata ya yi a saki Bazoum, amma mu ba za mu yi hakan ba. Amurka na taka tsantsan a kan haka, babu ma wani tunani game da far wa Nijar," in ji shi.

Jami'an Mali da Burkina Faso za su kai ziyara Nijar

A ɓangare guda kuma, Mali da Burkina Faso za su tura wani ayarin jami’ai na haɗin gwiwa zuwa Nijar don nuna goyon bayansu ga sojoji masu juyin mulki, da suka kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnati.

Rundunar sojin Mali ta ce manufar wannan ziyara ita ce nuna goyon bayan ƙasashen biyu wadanda suka haɗa iyaka da Nijar.

Ma’aikatar harkokin wajen Nijar ta ce a ranar Litinin ne ake sa ran ayarin zai sauka a ƙasar.

Mali da Burkina Faso, inda sojoji a can ma suka ƙwace mulki a shekarun 2020 da kuma 2022, sun yi gargaɗin cewa za su ɗauki matakin sojin da Ecowas za ta ɗauka a kan Nijar a matsayin wata shelar yaƙi.