Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Martanin gwamnonin APC na Najeriya kan zabar Shetima mataimakin Tinubu
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon: Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya na jam'iyyar APC sun musanta rahotannin da ke cewa ba su ji daɗi ba da ɗan takaran shugaban ƙasa na jam'iyyar, wato Bola Tinubu ya ɗauki Kashim Shetima a matsayin abokin takararsa maimakon daya daga cikinsu.
A tattaunawarsu da Ibrahim Isa, gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya ce suna goyon bayan zabin da aka yi wa Kashim Shetima, kuma za su tsaya wajen ganin jam'iyyar ta yi nasara a babban zaben da ke tafe.
Sai dai ya fara ne da kare hadin da jam'iyyar APC ta yi na Musulmi da Musulmi a matsayin dan takaran shugaban kasa da mataimakinsa.