Yadda ake gyaran jiki da turaren wuta a Maiduguri

Bayanan bidiyo, Yadda ake sana’ar gyaran jiki da turaren wuta a birnin Maiduguri
Yadda ake gyaran jiki da turaren wuta a Maiduguri
An wallafa

Sana'ar gyaran jiki, sana'a ce da ta jima musamman tsakanin al'ummar Kanuri da ke arewa maso gabashin Najeriya musamman Maiduguri da sauran garuruwan yankin.

Akan yi wa mata musamman sabbin amare gyaran jiki da turaren wuta domin su ɗauki hankalin ango.

Hajiya Maryam Muhammad da ke sana'ar ta ce takan samu kayayyakin haɗa kamshin ne daga wurare daban-daban a faɗin duniya.

Sannan kuma takan aika kayayyakinta da take sayarwa zuwa yankunan da dama na faɗin duniya ciki har da China.