Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dangin mutanen da suka faɗo daga jirgin Amurka a Afghanistan na son a ba su diyya
Dangin mutanen da suka faɗo daga jirgin Amurka a Afghanistan na son a ba su diyya
An wallafa
A shekarar da ta wuce, wani yamutsi da ya faru a filin jiragen saman Kabul da ke kasar Afghanistan, ya ja hankalin kasashen duniya.
Yamutsin ya faru ne yayin da dubban 'yan kasar suke kokawar shiga jirgin saman sojin Amurka domin ficewa daga Afghanistan, yayin da kungiyar Taliban ta kwace kasar.
A yayin da jirgin ya tashi, mutane da dama da suka ɗafe shi sun faɗo daga samansa inda suka mutu.
Ma'aikacin BBC Pashto Yama Bariz ya kai ziyara gidan iyalan wani da ya faɗo daga kan jirgin lamarin da ya yi sanadin mutuwar a Kabul, inda suka bukaci a yi adalci game da mutuwar ɗan nasu.