Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Mustapha, mataimakin Farfesa Maqari

Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Mustapha, mataimakin Farfesa Maqari
An wallafa

Filin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Sheikh Muhammad Mustapha Yusuf Shuaib, wani malami a birnin Kano da ke Najeriya.

An haife shi ne a unguwar Kurnar Asabe ta karamar hukumar Fagge a 1979.

Ya bayyana cewa ya soma karatunsa na addini a wurin mahaifinsa, wanda malamin addini ne, amma daga bisani aka mika shi a hannun almajirinsa Sheikh Abdulmajid, inda a nan ya yi karatun Alkur'ani zuwa izifi goma sha biyu.

Ya kara da cewa a 1991 mahaifin ya kai shi Bauchi wurin fitaccen malamin nan Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin ya ci gaba da karatun addini.

Sheikh Muhammad Mustapha ya kara da cewa daga Bauchi ya koma Kano makarantar Sheikh Manzo Arzai inda ya kammala haddace Alkur'ani da tilawa da sauran karatun addini.

A 2002 ya shiga makarantar koyon aikin Shari'a ta School of Legal Studies da ke Kano ina ya karanci kimiyya Alkur'ani wato Quranic Science inda ya kammala a 2004.

Malamin ya kuma tafi kasar Morocco inda ya karo karatu, kuma ya dawo Najeriya inda yanzu haka shi ne babban limamin masallacin Zone 5 da ke Abuja.

Sheikh Muhammad Mustapha, wanda kuma ya yi karatu a kasar Saudiyya, yana daya daga cikin mataimakan fitaccen malamin nan Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari.