Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdullahi, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zaria
Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdullahi, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zaria
An wallafa
Sheikh Abdullahi Abubakar Abba Zaria wanda mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zaria ne ya yi karatunsa na firamare da sakandare da jami'a duka a birnin na Zazzau.
Sheikh Abdullahi ya ce ya tasirantu da kakansa na wurin mahaifiya, wani shahararren malami ne inda ya zauna a zaurensa domin samun karatun al-Qur'ani.
Malam Abdullahi ya yi aiki a ƙungiyoyi masu zaman kansu daban-daban sannan ya yi aiki da asibitin fata da tarin tibi da ke Zaria.
Baya ga fannin addini, sheikh Abdullahi ya shiga siyasa inda yanzu haka shi ne mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zariya da ke jihar Kaduna.



