Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haaland da Bellingham sun shiga jerin ƴan wasan da ake so a karrama
Erling Haaland da Jude Bellingham suna daga cikin waɗanda aka zaɓa don samun kyautar wasannin duniya ta Laureus na 2024.
Manchester City na cikin ƙungiyoyin da za su iya lashe kyautar fitacciyar ƙungiya ta duniya kuma ɗan wasanta na gaba Haaland na cikin ƴan wasan da suka fi fice a bana.
Dan wasan tsakiya na Ingila da Real Madrid Bellingham da zakaran tseren mita 1500 na duniya Josh Kerr sun shiga cikin jerin sunayen waɗanda za su iya lashe kyautar.
Haaland, mai shekaru 23, ya ci ƙwallo 52 a wasanni 53 a kakar wasansa ta farko da City ta yi nasara a manyan gasanni uku inda ta lashe gasar Premier da kofin FA da kuma gasar zakarun Turai.
Bellingham, mai shekara 20, ya zama babban ɗan wasa a Real bayan da ya koma ƙungiyar daga Borussia Dortmund kan kuɗi Yuro miliyan 103 a bara, inda ya ci ƙwallo 20 a wasanni 29 a kakar wasa ta bana.
Za a gudanar da bikin bayar da kyautar ne a birnin Madrid na Sifaniya a ranar 22 ga watan Afrilun 2024.