Super Eagles ta ci Benin a wasan neman shiga gasar kofin Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tawagar ƙwallon kafa ta Najeriya ta doke ta Benin 3-0 a wasan farko a rukuni na huɗu a neman shiga gasar kofin Afirka da za a yi a Morocco a 2025.

Super Eagles ta fara cin ƙwallon ta hannun Ademola Lookman daf da hutu a karawar da suka yi a filin wasa na Goodswill Akpabio a Uyo da ke Akwa Ibom.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, Victor Osimhen ya kara na biyu, wanda ya koma Galatasaray, domin buga wasannin aro daga Napoli a makon jiya.

Saura minti bakwai a tashi daga karawar Lookman ya kara na uku a raga, inda Super Eagles ta haɗa maki uku da makinta uku a wasan farko a rukuni na huɗu.

Kyaftin din Najeriya, Ekong ya samu buga wasan, inda Victor Osimhen da Maduka Okoye suka fara da zaman benci.

Ranar Talata 10 ga watan Satumba, Najeriya za ta je Kigali, domin buga wasa na biyu a rukuni na huɗu da Rwanda a karawar neman zuwa Morocco a 2025.

Libya da Rwanda sun tashi 1-1, kenan Super Eagles ce ta ɗaya a rukunin da maki uku da ƙwallo uku a raga a wasan farko.

Ranar 10 ga watan Yuni Benin ta doke Najeriya 2-1 a wasan neman shiga gasar kofin duniya da suka fafata a rukuni na uku.

Wannan shi ne wasan farko da kociyan Najeriya, Augustine Eguavoen ya ja ragamar Super Eagles karo na uku jimilla, bayan 2010 da 2021.

Eguavoen ya maye gurbin Bruno Labbadia, wanda ya ci karo da cikas da hukumar ƙwallon kafar Najeriya, bayan da suka cimma yarjeniya tun farko.

Labbadia, wanda bai ja ragamar koda wasa ɗaya ba, ya maye gurbin Finidi George, wanda aka sallama, sakamakon da Benin ta doke Super Eagles 2-1.

Benin tana tare da tsohon wanda ya horar da Super Eagles, Gernor Rohr, wanda ya yi aiki tsakanin 2016 zuwa 2021.

Dan kasar Jamus ya ja ragamar Benin karawa ta 13 kenan, wanda ya yi nasara uku aka doke shi wasa shida kawo yanzu.

Benin tana ta uku da maki bakwai a rukuni na uku a neman gurbin shiga gasar kofin duniya, yayin da Super Eagles take ta biyar da maki uku, bayan fafatawa hur-huɗu a cikin rukuni.

Rwanda ce ta ɗaya da maki bakwai a rukuni na uku a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da kuma Mexico.