Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda masu laifi ke zaɓar yin yaƙi a Ukraine maimakon fuskantar shari'a a Rasha
- Marubuci, Olga Ivshina
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Da misalin ƙarfe 06:45 na ranar 28 ga watan Maris, ƴansanda sun isa gidan Andrey Perlov da ke kusa da Novosibirsk a Siberia. Ya tashi daga barci da sassafe domin zuwa ɗkin motsa jiki, amma aka aika ƴansandan suka dawo da shi gida domin su gudanar da bincike.
Sun zarge shi da satar kimanin dala miliyan 32,000 daga kungiyar ƙwallo ta Novosibirsk inda ya yi aiki a matsayin manajan kulob ɗin.
Iyalansa sun ce abin da ya yi shi ne barin yara su yi atisaye a filin wasa ba tare da biyan kuɗin da ya kamata su biya ba domin wasa a filin, sun dai biya kuɗi domin samun mai horaswa. Masu zargin sa da aikata laifi sun ce shi ma ya samu wani kaso na kuɗin.
Perlov wanda mai shekara 62 ne ya kasance ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Olympic inda kuma ya ɗauki lambar zinare bayan samun nasara a wani gudun kilomita 50 a 1992. An tsare shi tsawon fiye da watanni shida kuma iyalansa sun ce ana matsa masa ya amince zai yi yaƙi a Ukraine. An faɗa masa cewa idan ya koma ƙasar daga Ukraine to za a dakatar da tuhumar da ake yi masa ta almubazzaranci wato za a jingine shari'ar bayan kammala yaƙin.
“Ya ƙi amincewa inda muka kwarmata batun a kafafan watsa labarai na gida," kamar yadda ƴarsa Alina ta faɗa, "hakan ne ya sa aka sa shi bayan kanta, inda suka kuma sake tunkarar sa da wannan buƙata." Alina ta ƙara bayani cewa lokacin da ya ƙi amince wa da buƙatar a karo na biyu, sai aka haramta masa gani ko kiran iyalansa.
Ba ɓoyayyen abu ba ne cewa an tirsasa fursunoni shiga yaƙi a Ukraine, amma kuma wani sharhin BBC ya iya gano yadda aka sauya tsarin daga fursunonin masu ɗauke da manyan laifuka. Dokar baya-bayan nan na nufin cewa dukkannin masu shigar da ƙara da lauyoyin waɗanda ake ƙara yanzu dole ne su bi dokar sanar da duk mutumin da ake zargi da aikata ayyukan ɓatagari sun da zaɓin zuwa yaƙi maimakon tsayuwa a kotu.
Dokar wadda aka rattaɓa wa hannu a watan Maris 2024, na nufin idan mutum ya amince da zuwa yaƙin to za a jingine duk wata shari'a a kansa. Za a rufe tuhumar da ake yi musu a ƙarshen yaƙin.
"Wannan ya sauya tsarin tabbatar da doka a ƙasar," in ji Olga Romanova, darektar mutanen da ke kurkuku a Rasha, wata ƙungiya mai zaman kanta da ke taimaka wa fursunoni ta hanyar shari'a.
Yanzu haka ƴansanda za su iya kama mutum bisa zargin kisan wani. Amma da zarar mutmin da suka kama ɗin ya ce ku tsaya zan je yaƙi Ukraine. To kawai sai a kwance masa ankwa kuma a jingine tuhumar da ake yi masa."
Mun samu wata muryar wani mai bincike da ke bayyana alfanun rattaɓa hannu da sojojin Rasha ga matar da aka riga aka yanke wa mijinta hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku bisa sata.
Idan wanda ake tuhumar ya rattaɓa hannu, a cikin ƴan kwanaki za a rufe tuhumar da ake yi masa, kuma za a saki mutumin domin tafiya filin daga a Ukraine cikin gaggawa. Wasu lauyoyi guda uku da ke aiki a Rasha sun tabbatar da cewa wannan ya zama al'ada a ƙasar yanzu haka.
Wasu masu laifin kan amince da dokar bisa fatan da suke da shi na guje wa zaman gidan yari da kuma ɓata suna, amma kuma hakan ba abu ne mai sauƙi ba, kamar yadda wani matashi Yaroslav Lipavsky ya gano. Ya rattaɓa hannu a yarjejeniyar bayan da aka zarge shi da "cutar da mutane da ganganci".
Budurwarsa ta gano cewa tana ɗauke da juna biyu kuma a fatansa na ƙyamar zaman gidan kaso sai ya rattaɓa hannu a kan yarjejeniyar da sojoji a lokacin da ya cika shekara 18 da haihuwa.
Ya bar kasar zuwa Ukraine kuma bayan mako guda an kashe shi - inda ya kasance ɗaya daga cikin sojoji masu ƙarancin shekaru da aka kashe a yaƙin.
Babu dai tabbas dangane da mutum nawa ne da ake zargi da aikata ayyukan ɓata gari suka zaɓi zuwa yaƙi maimakon tsayawa gaban alƙali, to amma wannan tsari yana nuni da buƙatar Rasha na ƙara yawan dakarunta a daidai lokacin take koƙarin rage amfani da fararen hula a yaƙin.
A lokacin da ƙungiyar dakarun Wagner ta fara ɗibar fursunoni a matsayin mayaƙa, shugabanta na lokacin marigayi Yevgeny Prigozhin ya mayar da hankali ga fursunoni masu manyan laifuka, inda ya ce yana buƙatar "basirarsu ta aikata laifi" domin a yi musu afuwa.
Shafukan BBC da na Mediazona na Rasha sun ga wasu takardun sirri da suka yi ƙarin haske kan tsarin dibar fursunoni domin yin yaƙi, da abin da ya faru da dama daga cikinsu da kuma buƙatar da ƙasar ke da akwai na samar da ƙarin mayaƙa.
Mun gano daga alamu da kuɗaɗen makara da aka bai wa iyalan fursunonin da aka kashe a Ukraine, waɗanda Wagner ta ɗauka aiki kusan 50,000, inda a wani lokaci ma su kan kai kusan mutum 200 da ke aiki a kullum. An jikkata da dama daga cikinsu.
Dukkannin alamun fursunonin sun fara ne da baƙin L wanda ke nufin "kolonya" ko kuma daular gidan yari. Lambobi uku na farko sun bayyana gidan yarin da suka fito sannan kuma lambobin uku na ƙarshe suna nuni da yawan fursunonin da suka fito daga kowacce daular gidan yari.
Bayanan kuɗin makara sun nuna cewa an kashe fursunoni fiye da 17,000 a ƙokarinsu na kama birnin Bakhmut a gabashin Ukraine tsakanin watan yulin 2022.
Ƙungiyar Wagner tare da ma'aikatar tsaron Rasha sun rungumi tsarin ɗaukar fursunonin aikin soji domin ƙara yawan hanyoyin samun mayaƙa.
Wasu mutane da ake zargi da kin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar saboda suna ƙin yaƙin da ake yi Ukraine, inda wasu kuma suka ƙi yin hakan saboda tsoron mutuwa ko kuma samun rauni a fagen daga sannan wasu kuma sun ƙi yin hakan ne saboda ƙaunar da suke ga zaman gida.
Iyalan Andrev Perlov dai har yanzu na nuna cewa bai aikata laifin da ake tuhumar sa ba, amma kuma lokaci na ƙarshe da Alina ta ga mahaifinta a kotu a watan Yuli ya rame sosai. "Ya yi ƙoƙarin nuna yana cikin farin ciki," in ji ta, "amma suka faɗa masa cewa idan ya ci gaba da haka za su karya shi."
Mun tambayi hukumomin Rasha dangane da Andrey Perlov da kuma ko suna tursasa wa fursunoni su shiga aikin soji - ba su ce uffan ba.