Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man U da City da Madrid na fafatawa kan ɗan shekara 15, Ten Hag zai ci gaba da zama daram
Chelsea na son dauko dan wasan New York Red Bulls dan kasar Amurka Julian Hall, mai shekara 15, amma suna fuskantar hamayya daga Manchester United, da Manchester City, da Real Madrid da Bayern Munich don zawarcin dan wasan. (Standard)
Manchester United da Manchester City za su fafata wajen neman dan wasan Brighton dan kasar Japan Kaoru Mitoma mai shekaru 26 a watan Janairu. (Fichajes Spanish)
Sai dai kungiyoyin biyu na Manchester na iya yin rashin nasara kan wannan aniya ta su, domin kuwa Mitoma na shirin kulla sabuwar yarjejeniya ta dogon lokaci da Seagulls. (London World)
Babu wata barazana ga Erik ten Hag a matsayin kocin Manchester United har nan da wani tsawon lokaci, duk da rashin nasarar da kungiyar ke yi a kakar wasa ta bana. (Guardian)
Dan wasan kasar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg yana son barin Tottenham idan har kungiyar ba za ta iya ba shi damar buga wasa ba, yayin da Juventus ke zawarcin dan wasan mai shekaru 28. (Gazzetta)
Bayern Munich na shirin bai wa dan wasan bayan Canada Alphonso Davies, mai shekara 22, sabon kwantiragi domin dakile sha'awar da Manchester City, da Chelsea da Real Madrid ke nunawa kan dan wasan. (90 Mints)
Dan wasan Bayern Leroy Sane na iya barin kulob din a bazara mai zuwa, inda Barcelona da Real Madrid za su iya zawarcin dan wasan na Jamus mai shekara 27. (Bild Germany)
Fiorentina na shirin bai wa dan wasan bayan Italiya Michael Kayode sabon kwantiragi yayin da Arsenal ke nuna sha'awar dan wasan mai shekaru 19. (Calcio Mercato)
Chelsea na sa ido sosai kan halin da dan wasan tsakiyarta na Brazil Andrey Santos ke ciki a Nottingham Forest kuma za ta iya dawo da abunta gida idan har ba a fara wasa da shi. (The Athletic)
Dan wasan tsakiyar Athletic Club na Spain Nico Williams na gab da cimma sabuwar yarjejeniya, da za ta kawo karshen fatan Brighton da Aston Villa na sayen dan wasan mai shekaru 21. (Sport Spanish)
Arsenal da Liverpool da kuma Manchester United na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan Feyenoord dan kasar Holland Quinten Timber mai shekaru 22 a duniya. (90 Mints)
Dan wasan gaba na Ingila Ivan Toney na tunanin barin Brentford a watan Janairu, inda Tottenham ko Chelsea za su iya zawarcin dan wasan mai shekaru 27. (Insider Football)
Burnley na zawarcin dan wasan tsakiya na kungiyar Millwall mai shekara 18 Romain Esse. (Talk)