Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ba ta tsawaita kwantiragin Alonso ba
Marcos Alonso ba zai ci gaba da taka leda a Barcelona, bayan da ƙungiyar ba ta tsawaita masa kwantiragi ba.
Yarjejeniyar ɗan ƙwallon mai tsaron baya, ya kare a Barcelona a karshen watan Yuni, wato ranar Lahadi 30 ga watan.
Mai tsaron bayan ya koma Barcelona daga Chelsea a 2022, wanda ya ci ƙwallo uku a karawa 45.
Alonso ya buga wa Barcelona wasa 45 a kaka biyun da ya yi a ƙungiyar.
Ɗan kasar Sifaniya ya buga wa Barcelona wasa takwas a kakar da ta kare - karawa biyar a La Liga da uku a Champions League.
Mai tsaron bayan yana fama da jinyar ciwon baya - hakan ya sa baya samun buga wasanni sosai.
Wasu rahotanni na cewar Alonso na nazarin ƙungiyar da ya kamata ya koma da taka leda, har ana alakanta shi da Atletico Madrid.
Tuni kuma Barcelona ta amince da ɗan ƙwallon Amurka, Sergino Dest ya koma PSV Eindhoven, wadda ya buga wa wasannin aro - kwantiraginsa ya kare 30 ga watan Yuni.
Ɗan ƙwallon ya taka rawar gani a gasar ta Netherlands da aka kammala, sai dai ya ci karo da koma baya sakamakon raunin da ya ji a cikin watan Afirilu.