Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
De Bruyne da Laporte ba su yi wasan Man City da Leipzig ba
Manchester City ta tashi 1-1 da RB Leipzig a wasan farko zagayen 'yan 16 a Champions League da za su kece raini a Jamus ranar Laraba.
Minti na 27 da take Leda City ta ci kwallo ta hannun Riyad Mahrez, yayin da Leipzig ta farke ta hannun 'Josko Gvardiol a minti na 70.
Sai dai Kevin de Bruyne da Aymeric Laporte ba su buga wa City wasan ba.
'Yan wasan biyu ba su yi atisaye ba ranar Talata, hakan ne ya sa ba a bayyana su cikin wadanda kungiyar ta je da su Jamus ba.
Pep Guardiola ya ce 'yan kwallon na fama da rashin lafiya, shi ya sa bai je da su Leipzig ba.
Shima John Stones bai yi wasan ba, wanda ke jinya, amma sabon dan kwallon da ta dauka a Janairu, Maximo Perrone ya bi kungiyar zuwa Jamus.
Ranar 25 ga watan Maris za su buga wasa na biyu a Etihad.