Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
A karon farko Araujo zai fara buga wa Barcelona wasa a bana
Barcelona za ta karɓi baƙuncin Leganes a La Liga ranar Lahadi a fafatawar mako na 18.
Ana sa ran a karon farko a bana, Ronald Araujo zai yi wa Barcelona wasa, bayan jinyar wata shida.
Tuni koci, Hansi Flick ya sanar cewar watakila ya sa Araujo cikin 11 da zai fara fuskantar Laganes, domin samun maki uku ranar Lahadi.
Mai shekara 25, mai tsaron raga ya ji rauni ne a wasan da Uruguay ta doke Brazil a kwata fainal a cikin watan Yuni.
Ana tunanin Flick zai ke canja ƴan wasansa, domin shawo kan matsalar koda wani ya ji rauni ana da madadinsa a kasa.
Sai dai kociyan ba kasai fai yake canja ƴan wasa ba, kamar yadda ya horar a Bayern Munich, sai dai tarin matasan da yake da su a Barcelona ya sa ya rungumi sauye-sauyen.
Barcelona tana matakin farko a kan teburin La Liga da maki 38, sakamakon da ta ci wasa 12 da canjaras biyu aka doke ta karawa uku.
Tana da tazarar maki biyu kenan da Real Madrid mai biye da ita, wadda take da ƙwantan wasa.
Ita kuwa Leaganes tana ta 17 a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da maki 16