'Sai na kori baƙi daga Amurka'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Donald Trump ya ƙara jaddada matsayar sa a kan kwararar baƙi cikin Amurka, inda ya sha alwashin aiwatar da manufar sa ta fatattakar baƙi ''mafi girma a tarihi'', idan ya sake zama shugaban ƙasa.

A hirar da ya yi kai tsaye da shugaban shafin sada zumunta na X, Elon Musk, Mr Trump ya yi ƙarin haske kan matsayar sa game da ɓaki masu shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba, da kuma yunkurin kashe shi da aka yi.

An ɗan samu tsaiko kafin fara tattaunawar da ɗinbin jama’a suka yi ta jira domin sauraro a shafin X.

Shi dai Mr Elon Musk ya alaƙanta jinkirin da aka samu ne da yunƙurin yin kutse da ya ce wasu sun riƙa yi cikin shafin, a daidai lokacin da ake shirin fara tattaunawar.

Ɗan takarar shugabancin Amurkan a jam’iyyar Republican, ya shaidawa hamshakin attajirin cewa ba zai yi wata-wata ba, wajen zartar da korar baƙi mafi girma a tarihi, idan har ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a watan Nuwamba mai zuwa.

Mr Trump ya ce ba gudu babu ja da baya a shirin sa na gina katangar da za ta zamo shinge domin kare ƙasarsa daga kwararar baƙin da za su zame mata barazana.

Ya ce: "Aikata laifi ya ragu a duniya baki ɗaya, kuma ka jira tukun sai ka ga alƙalumman da muke da su. Wannan babban laifi ne, shiga ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ƙara da cewa ''Mutane ne abin tsoro. Mutane ne da aka tura gidan yari saboda aikata kisan kai da sauran manyan laifuka, kuma sun zo suna turo mana su cikin ƙasar mu, suna kuma gargaɗin su cewa idan har suka koma za a kashe su.

Kodai za a yanke masu hukuncin kisa ko kuma a kashe su nan take, idan har suka koma ƙasashen nasu. Waɗan nan fa masu laifi ne da tsananin laifin su ya sa muke kallon namu masu laifin kamar ba masu laifi ba, abinda suke aikatawa ya yi muni sosai.’’

An dai yi wannan tattaunawa ne bayan abokiyar hamayyar Donald Trump, Kamala Harris, ta shige gabansa a ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a.

Mr Musk ya fito fili ya bayyana goyon bayan sa ga Mr Trump ne bayan an yi yunkurin kashe tsohon shugaban Amurkan a wajen yakin neman zaɓe a watan jiya.

A ranar Litinin Donald Trump ya koma amfani da shafin X, a karon farko cikin kusan shekara guda, kuma ya wallafa saƙonni bidiyo na neman zaɓen sa.