Kocin Betis, Pellegrini ya kware wajen cin Man United

An wallafa

Koci, Manuel Pellegrini shine zai ja ragamar Real Betis buga wasa da Manchester United a Europa League ranar Alhamis a Old Trafford.

United da Betis za su buga wasan farko zangon 'yan 16 a Europa League a kakar bana.

Mai shekara 69 dan kasar Chile ya yi kaka uku a Manchester City tsakanin 2013 zuwa 2016 ya kuma yi West Ham United.

Pellegrini ya kalli minti 45 a wasan da Liverpool ta doke United 7-0 a gasar Premier League ranar Lahadi.

Kociyan ya fuskanci United sau 13, karawa uku kacal aka doke shi,, wanda ya ci biyar da canjaras biyar

Haka kuma Pellegrini – shine mai horarwa tilo da ya yi nasara a kan kociyan United hudu a tarihi.

Dan kasar Chile ya doke Ole Gunnar Solskjaer da Jose Mourinho da Louis van Gaal da kuma David Moyes dukkansu a United.

Haka kuma Pellegrini ya yi canjaras hudu da ya fuskanci Alex Ferguson a Champions League a lokacin da ya horar da Villareal

Pellegrini ya yi nasara uku daga wasa shida a baya nan a lokacin yana Etihad har da cin United 3-0 a Old Trafford a 2014.

Betis tana mataki na biyar a La Liga, wadda ta tashi 0-0 da Real Madrid ranar Lahadi a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Kungiyoyin da Pellegrini ya horar:

1988–1989 Universidad de Chile

1990–1991 Palestino

1992–1993 O'Higgins

1994–1996 Universidad Católica

1998 Palestino

1999–2000 LDU Quito

2001–2002 San Lorenzo

2002–2003 River Plate

2004–2009 Villarreal

2009–2010 Real Madrid

2010–2013 Málaga

2013–2016 Manchester City

2016–2018 Hebei China Fortune

2018–2019 West Ham United

2020– Real Betis