Girke-girken Ramadan: Yadda ake wainar Oats da miyar kaza

Bayanan bidiyo, Girke-girken Ramadan
Girke-girken Ramadan: Yadda ake wainar Oats da miyar kaza
An wallafa

Wannan wani shiri ne da BBC Hausa ke kawo muku kullum a cikin watan azumi don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.

A wannan bidiyon za ku kalli yadda ake haɗa wainar Oats da miyar kaza, girkin da gwanar tamu ta ce ko masu olsa da hawan jini suna iya ci ba tare da matsala ba.

Chef Raja wadda aka fi sani da diaryofanortherncook a shafin Instagram, wata ƙwararriyar mai girki ce kuma ta nuna mana yadda ake wannan haɗi mai ƙayatarwa.