Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United za ta kara da Sevilla a Europa League
Manchester United za ta karbi bakuncin Sevilla a wasan farko matakin quarter finals a Europa League ranar Alhamis a Old Trafford.
Kungiya ta hudu daga Sifaniya da United za ta fuskanta a gasar ta zakarun Turai a kakar nan.
Tun farko United ta kara da Real Sociedad a cikin rukuni, inda kungiyar Sifaniya ta yi ta daya, United ta yi ta biyu.
Hakan ya sa kungiyar Old Trafford ta buga wasan cike gurbin zuwa zagaye na biyu a Europa League, wadda ta fitar da Barcelona.
A karawar zagaye na biyu kuwa, United ta yi waje da Real Betis, hakan ya sa ta kawo matakin quarter finals da za ta kece raini da Sevilla.
Ita kuwa Sevilla Fernabahce ta fitar a zagaye na biyu, shi ya sa ta samu gurbin fuskantar United a quarter finals.
Wasa na hudu da za su buga a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Sevilla ta yi nasara biyu da canjaras daya.
Manchester United tana mataki na hudu a teburin Premier League, ita kuwa Sevilla tana ta 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Sevilla ce kan gaba a tarihin lashe Europa League mai shida jimilla, ita kuwa United daya take da shi, wanda Jose Mourinho ya daukar mata a 2016/17 tare da League Cup.
Tun daga lokacin kofi ya yi wa United wahalar dauka, sai a bana da Erik ten Hag ya ci Carabao Cup ya kuma kai daf da karshe a FA Cup da zai fuskanci Brighton.
To sai dai Marcus Rashford ba zai buga wa Manchester United wasan ba, sakamakon jinya da zai yi.
Mai shekara 25 dan kwallon tawagar Ingila ya ji rauni ranar Asabar a karawar da United ta ci Everton a wasan Premier League.
United ba ta fayyace kwanakin da zai yi jinya ba, illa ta ce zai murmure ya buga mata tamaula kafin karshen kakar nan.
Rashford mai kwallo 28 a bana ya buga wa United dukkan karawar lik a 2022/23.
Ten Hag zai yi amfani da Martial, mai shekara 27, wanda ya ci kwallo bakwai a karawa 17 da ya yi wa United a kakar nan.
Dan wasan tawagar Faransa na shan suka kan yawan jinya da yake yi, wanda ya shiga wasa sauyi sau uku har da karawa da Everton ranar Asabar da cin kwallo.
Haka shima Alejandro Garnacho na jinya, watakila, Luke Shaw ba zai yi wasan ba, amma Ten Hag na fatan zai murmure da wuri.
Har yanzu United ce kadai ke takara kofi uku kawo yanzu a bana, bayan da ta lashe Carabao Cup za ta buga daf da karshe a FA Cup da Brighton a Wembley.
Za ta kara da Sevilla a quarter finals a Europa League ranar Alhamis tana mataki na hudu a Premier League da kwantan wasa mai maki 56.
Wasa tskanin kungiyoyin biyu:
Europa League Lahadi 16 ga watan Agustan 2020
- Sevilla 2 - 1 Man Utd
Champions League Talata 13 ga watan Maris 2018
- Man Utd 1 - 2 Sevilla
Champions League Laraba 21 ga watan Fabrairun 2018
- Sevilla 0 - 0 Man Utd