Matashin ɗan majalisar wakilai da ya gaji mahaifinsa a jam'iyyar NNPP

Matashin ɗan majalisar wakilai da ya gaji mahaifinsa a jam'iyyar NNPP
An wallafa

Abdulhakim Kamilu Ado, sabon ɗan majalisar tarayya ne mai wakiltar Wudil da Garko, ya yi nasara ne a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, jim kaɗan bayan an ɗauke shi don yin takara a madadin mahaifinsa da ya rasu, makonni ƙalilan bayan ya ci zaɓen fid da gwani.

A wannan zantawa, Abdulhakim Ado ya ce karo na biyu kenan, da irin wannan al'amari yake zuwar masa bagatatan a rayuwa.