Ba ni da tabbas ko zan ci gaba da zama a Liverpool - Van Dijk

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙyaftin ɗin Liverpool, Virgil van Dijk ya ce ''bai da tabbas'' ko zai ci gaba da zama a Liverpool bayan karkare kakar nan.

Ɗan wasan tawagar Netherlands ɗaya ne daga fitattu uku a ƙungiyar da yarjejeniyar su za ta kare a karshen watan Yuni tare da Mohamed Salah da kuma Trent Alexander-Arnold.

An daɗe ana tattaunawa da Van Dijk, kuma mai tsaron bayan mai shekara 33 ya sanar a baya cewar a shirye yake ya tsawaita zamansa a Anfield.

To sai dai bayan da Paris St Germain ta fitar da Liverpool daga Champions League ranar Talata, sai ya jefa shakku kan makomarsa a ƙungiyar.

''Har yanzu ba ni da tabbas kan makomata,'' in ji Van Dijk.

''A yanzu haka ban san mai zai faru a shekara mai zuwa ba, duk wanda ya ce maka ya san mai zai faru, ya yi maka ƙarya kai tsaye.

''Kowa zai ce maka ana tattaunawa tsakani na da ƙungiyar, shi ne zancen ba daɗi ba ragi.''

Liverpool tana ta ɗaya a kan teburin Premier League da tazarar maki 15 tsakani da Arsenal, wadda take ta biyu.

Liverpol za ta kece raini da Newcastle United a Carabao Cup wasan karshe ranar Lahadi a Wembley.

An tambayi Van Dijk kan halin da ake ciki kan batun tsawaita zamansa a Liverpool, ko an jingine domin ya mayar da hankali a taka leda.

''Ba abin da aka dakatar. Ba a dakatar da komai ba, kamar yadda ya sanar.

''Saurara ka ji, saura wasa 10 ya rage a Premier League, kuma abin da na mayar da hankali na kenan, idan da wani labari za kuji.''