Yadda Najeriya za ta guje wa bala’in kwararowar hamada

Yadda Najeriya za ta guje wa bala’in kwararowar hamada
An wallafa

Zaizayar ƙasa da kwararowar hamada wasu tagwayen matsaloli ne da ke yin illa ga muhalli.

Wasu jihohin Najeriya na daga cikin yankin da ke buƙatar kariya game da wannan lamari.

Hukumomi a ƙasar sun kafa wata hukuma ta musamman wato 'National Agency for the Great Green Wall' don tunkarar waɗannan matsalolin, har ma da batun ɗumamar yanayi.

Shugaban hukumar, Saleh Abubakar ya ce hukumar na bayar da tallafin bishiyoyin da ake dasawa da 'ya'yan itatuwan da za a shuka masu muhimmanci da za a iya ci.

Ya ce hakan zai taimaka wajen samar da ayykan yi da sana'o'i.

Ya ƙara da cewa sare-saren itatuwa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalar kwararowar hamada a Najeriya.