Za mu fuskanci kalubale daga PSG - Van Dijk

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙyaftin ɗin Liverpool, Virgil van Dijk ya ce za su fuskanci karin kalubale fiye da wanda suka sha a Faransa a wajen Paris St Germain a Anfield.

Ranar Talata Liverpool, wadda ta je ta ci 1-0 a wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League a Faransa za ta karɓi bakuncin PSG ranar Talata.

Mai rike da Ligue 1 ta taka rawar gani a wasan farko, ita ce mai kaso mafi tsoka a rike ƙwallo da rabawa da kai hare-hare a Parc des Princes, amma aka doke ta.

Tuni ƙungiyar da Luis Enrique ke jan ragama ta sauka a Merseyside, wadda ta kwan da sanin jan aikin da ke gabanta na soke ƙwallon da aka zura mata a makon jiya.

''Ina jin ƙungiya ce mai ƙwazo, za kuma ka fahimci haka ta yadda ake gudanar da ita, in ji Van Dijk.

''Sun sa mana matsi sosai a Faransa, idan suka rasa ƙwallo suna tare yadda ya kamata sun kuma kai hare-hare da raba tamaula, haka muke sa ran za suyi a Anfield.''

''To amma a shirye muke, saboda kofunan da muke fatan lashewa a kakar nan har da na Champions League.''

A ranar Laraba da ta gabata a Faransa, Liverpool ta yi nasara ne a kan PSG sauran minti uku a tashi daga karawar ta hannun Harvey Elliott.

Shi ne karo na biyar da suka kara a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Liverpool ta yi nasara ta uku, Paris St Germain ta ci wasa biyu.

Wasan da aka buga tsakanin PSG da Liverpool:

2024/2025

Champions League ranar Laraba 5 ga watan Maris 2025

  • Paris St-Germain 0 - 1 Liverpool

2018/2019

Champions League ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba 2018

  • Paris St-Germain 2 - 1 Liverpool

Champions League ranar Talata 18 ga watan Satumbar 2018

  • Liverpool 3 - 2 Paris St-Germain

1996/1997

Euro Cup Winners Cup ranar Alhamis 24 ga watan Afirilun 1997

  • Liverpool 2 - 0 Paris St-Germain

Euro Cup Winners Cup ranar Alhamis 10 ga watan Afirilu 1997

  • Paris St-Germain 3 - 0 Liverpool