Abubuwan da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta ƙunsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken tare da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu suna gaisawa a Jerusalem.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken, ya ce akwai haske a ƙokarin da suke yi na tabbatar da an tsagaita wuta a yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza nan da wasu ƴan kwanaki bayan Isra'ila ta amince da buƙatar hakan ranar 19 ga Agusta.

Daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa, akwai daina kai hare-hare a Gaza, da kuma dawo da waɗanda Hamas ke riƙe da su tun bayan harin da suka kai a Oktoban 2023.

Amurka na ta ƙoƙarin samar da matsaya ne a kan abubuwan da suke jawo tsaiko a kan samun maslaha tsakanin Isra'ila da Hamas.

Waɗanne abubuwa yarjejeniyar ta Amurka ta ƙunsa?

Mista Blinken ya kwana biyu a Isra'ila, inda yake ta ƙoƙarin tabbatar da samun haɗin kan Isra'ila kan yarjejeniyar da Amurka ta tsara ƙarƙashin jagorancin Shugaba Joe Biden a watan Mayun bana.

Za a samar da yarjejeniyar ce a matakai uku.

Na farko shi ne "tsagaita wuta baki ɗaya" wanda zai ɗauki mako shida, janye sojojin Isra'ila daga dukkan yankunan Gaza masu ɗimbin mutane, da kuma musayar wasu waɗanda ake riƙe da su - ciki har da mata, da dattawa da marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni.

Za a yi musayarsu ne da wasu fursunoni ƴan Falasɗinu da suke riƙe da gidajen yarin Isra'ila.

Wani ƙaramin yaro daga cikin fursunonin yaƙin da ya dawo Isra'ila a Nuwamban 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Nuwamban 2023, fursunonin yaƙi 105 ne suka dawo Isra'ila, amma har yanzu akwai sama da 100 a Gaza.

Mataki na biyu shi ne sakin dukkan fursunonin yaƙi "baki ɗaya, da daina kai hare-hare."

Isra'ila ta ce akwai sama da ƴan ƙasarta 100 da ake riƙe da su, sannan ta yi amannar cewa 71 suna raye. Wasu fursunonin yaƙin huɗu dama suna Gaza tun kafin a fara yaƙin na 7 ga Oktoba, amma ana tunanin biyu daga cikinsu sun mutu.

Wata yarjejeniya da aka yi a Nuwamban 2023 ce ta sa Hamas ta saki fursunonin yaƙin 105, inda ita kuma aka sako mata Falasɗinawa 240 da suke gidajen yarin Isra'ila.

Hoton yadda aka ragargaza garin Gaza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daga matakan tsagaitar wutar akwai sake gina Gaza.

Mataki na uku shi ne sake gina birnin Gaza, da kuma dawo da gawarwakin fursunonin yaƙi.

A wata sanarwa da gwamnatin Isra'ila ta fitar a ranar 19 ga Agusta, ta ce, "Firaministan Isra'ila ya nanata shirinsa na goyon bayan shirin Amurka na tabbatar da yarjejeniyar na sakin fursunonin yaƙi, wanda yake cikin shirin ƙasar na tabbatar da tsaron ƙasar, wanda yake cikin ƙudurorinsa."

Waɗanne abubuwa ne suka fi muhimmanci a cikin yarjejeniyar?

Ana tunanin har yanzu akwai wasu saɓanin fahimta tsakanin Isra'ila da Hamas.

Daga ciki akwai cigaba da kasancewar sojojin Isra'ila a Gaza.

Ita kuma ta ce tana so sojojinta su cigaba da zama domin gudun kada Hamas ta samu damar sake shiri, da kuma hana ta samun ƙarin makamai.

Amma ita Hamas ba ta amince da cigaba da zaman sojojin ba a Gaba bayan ƙarewar wa'adin yarjejeniyar.

Haka kuma akwai saɓanin a kan yawan Falasɗinawa da Isra'ila ke riƙe da su da za su dawo Gaza domin musayarsu da waɗanda Hamas ke riƙe da su.

Sojojin Isra'ila suna sinitiri a cikin Gaza.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hamas ba ta yarda da cigaba da zaman sojojin Isra'ila ba a Gaza bayan an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ko akwai alamar nasarar cimma yarjejeniyar zaman lafiya?

Mista Blinken ya ce dole a cimma yarjejeniyar tsagaita wutar a cikin ƙanƙanin lokaci.

"Wannan wani lokaci ne mai muhimmanci, wataƙila ma lokaci ne mafi muhimmanci ko kuma ma na ƙarshe domin tabbatar da tsagaita wuta, domin ɗora dandamalin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa," inji shi a ranar 19 ga Agusta a Isra'ila.

Bayan ya samu haɗin kan gwamnatin Isra'ila, sai ya tafi birnin Alkahira na Masar domin ganawa da masu shiga tsakani na Masar da Qatar, waɗanda suke da hanyar isar da saƙo zuwa ga Hamas.

Ƴan Isra'ila suna zanga-zangar kira da a yi yarjejeniyar zaman lafiya domin a sako fursunonin yaƙi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da dama a Isra'ila na matsa wa gwamantin ƙasar lamba a kan ta tabbatar ta shiga yarjejeniyar domin ƴan uwansu su dawo.

Sai dai Hamas ta ce ba za ta aiki wakilai zuwa wajen ba.

Wani mamba a cibiyar tsare-tsaren siyasar ƙungiyar mazaunin Qatar, Basem Naim ya ce: "Mun amince da yarjejeniyar (ta hanyarr masu shiga tsakani) ranar 2 ga watan Yuli, don haka ba sai mun sake zama domin domin sake tattauna wasu buƙatun Benjamin Netanyahu ba.”

Ya ce Hamas a shirye take ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya, amma sai ya ƙara da cewa: "Mun bayyana kwarin gwiwarmu da sauƙin kanmu, amma sai ɗayan ɓangaren ya kalli hakan a matsayin gazawa - bai shirya tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ba - kuma ya fi ba buƙatun son ransa da siyasa muhimmanci,"

Gwamnatin Isra'ila ta mayar da martani ga Hamas, inda ta ce ƙungiyar na da taurin kai, kuma, "sai an sa mata ƙarfi."

Wani sojan Isra'ila a tsaye a bakin shiga wata hanyar ƙarƙashin ƙasa na Hamas a Gaza.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila na cigaba da ganowa tare da lalata hanyoyin ƙarƙashin kasa na Hamas.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare ne a Gaza domin mayar da martanin harin da Hamas ta kai mata a Kudancin ƙasar a ranar 7 ga Oktoba, inda aka kashe kusan mutum 1,200, sannan aka kama mutum 251 a matsayin fursunonin yaƙi.

Zuwa yanzu, an kashe sama da mutum 40,130 a Gaza kamar yadda Ma'aikatar Lafiyar yankin, wadda ke ƙarƙashin Hamas ta bayyana.

Har yanzu ana cigaba da yaƙin, inda Isra'ila ta sanar da cewa a ƴan makonnin da suka gabata ta lalata hanyoyin Hamas na ƙarƙashin ƙasa da dama, inda ta samu makamai masu linzami a ciki da rokoki, sannan, "an kashe gomman ƴan ta'adda."

Kafofin yaɗa labarai a Falasɗinu sun nuna cewa a ranar Litinin, wani harin Isra'ila ya kashe mutum shida a Khan Younis, a Kudancin Gaza, sannan kuma an kashe mutum ƙarin mutum huɗu a wani harin da aka kai a kan wata mota a Gaza.

A daidai lokacin da Mista Blinken yake cigaba da bayyana cewa an kusa cimma matsaya, dukkan majiyoyin Isra'ila da Hamas da BBC ta nema domin jin ta bakinsu, ba su da irin wannan ƙarfin gwiwar.