Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bambanci biyar tsakanin ƙyandar biri da korona
- Marubuci, Dorcas Wangira
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa health correspondent
- Aiko rahoto daga, Nairobi
- Marubuci, Carolyne Kiambo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa health producer
- Aiko rahoto daga, Nairobi
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana ƙyandar biri (mpox) a matsayin cuta mai barazana ga lafiyar ɗan'adam karo na biyu a cikin shekara biyu, mutane da dama sun yi tambayar cewa: ko wannan ce cutar korona ta biyu?
Masana kimiyya sun ce tabbas wannan tambaya ce mai ƙwari sai dai amsar ita ce a'a.
Mpox ba sabuwar korona ba ce. Hatsarinta ga al'umma bai kai na korona ba," in ji Dr Hans Kluge, daraktan Hukumar WHO a yankin Turai.
"Mun san yadda za mu dakatar da mpox. A yankin Turai mun san matakan da za mu ɗauka domin hana yaɗuwarta baki ɗaya."
Ƙwayoyin cutar bairos 'virus' ne ke haifar da cutukan biyu, amma alamomin kamuwa da su sun sha bamban, kuma yadda suke yaɗuwa ya sha bamban.
"Bambancinsu sun fi fitowa ƙarara a kan kamanceceniyarsu," in ji farfesa Rodney Adam, babban masanin cutuka masu yaɗuwa a asibitin Aga Khan da ke Kenya.
Ga bambance-bambance biyar da ke tsakanin cutukan biyu.
1. Ƙyandar biri ba sabuwar cuta ba ce
Ƙyandar biri (Mpox), wanda a baya ake kira 'monkeypox' a turance cuta ce da ta daɗe, tun shekarar 1958, lokacin da aka fara gano cutar a jikin birai da ake tsare da su a ƙasar Denmark.
An fara samun mutumin da ya kamu da cutar ne a Jamhuriyar Demokuraɗiyyra Kongo a shekarar 1970.
Tun daga wancan lokaci an riƙa samun ɓarkewar cutar a ƙasashen Yammaci da kuma Tsakiyar Afirka.
An fara ayyana cutar a matsayin barazana ga lafiya a duniya ne a shakarar 2022, cutar ta yaɗu a sama da ƙasashe 70.
Ita kuwa cutar korona wadda ta ɓulla a 2019 a birnin Wuhan na ƙasar China, wadda nan-da-nan ta zama annoba a duniya, wata ƙwayar cuta ce da ake kira SARS-CoV2 - wadda ba a taɓa samun irin ta tsakanin mutane a doron ƙasa ba.
Masana kimiyya sun ce a yanzu ana da masaniya sosai kan cutar mpox fiye da cutar korona a lokacin da aka ayyana ta a amtsayin annoba.
2. Mpox bai da saurin yaduwa kamar korona
Duk da cewa dukkanin cutukan biyu na yaɗuwa ne sanadiyyar cuɗanya a kusa da juna, korona ta fi saurin yaɗuwa kasancewar tana bin iska ne.
Mutum zai iya kamuwa da ita idan ya shaƙi ƙananan ƙwayoyin da mai ɗauke da cutar ya fitar ta hanyar tari ko atishawa ko magana ko waƙa, ko ma shaƙara numfashin mai fama da cutar, in ji Hukumar WHO.
Ita kuwa mpox tana yaɗuwa ne ta hanyar cuɗanya ta ƙut da ƙut ko cuɗanya ta tsawon lokaci da mai ɗauke da cutar, kamar haɗa jiki, kamar saduwa, kwanciya a kan gadon da mai cutar ya kwana ko sanya tufafinsa ko kuma zama gaba-da-gaba da mai cutar na tsawon lokaci.
Sama da mutum miliyan 760 ne suka kamu da korona a fadin duniya tsakanin watan Disamban 2019 zuwa Agustan 2023, in ji WHO, yayin da a ɓangare ɗaya sai da aka kwashe shekara biyu, daga watan Mayun 2022 kafin yawan waɗanda suka kamu da cutar mpox su kai 100,000 a faɗin duniya.
A shekarar 2024, Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaduwa ta Afirka (CDC) ta samu mutum 18,910 da suka kamu da cutar yayin da kimanin mutum 600 suka mutu.
3. Akwai rigakafin mpox
A lokacin da korona ta bayyana an ta fafutikar yadda za a nemo rigakafinta. Amma yanzu gaka akwai rigakafin cutar mpox.
Kyandar biri na da alaka ne da cutar farankama, cutar da duniya ta ga bayanta ta hanyar rigakafi a shekarar 1980.
Rigakafin da ta yi aiki kan farankama tana kuma bayar da kariya daga kyandar biri, musamman ma lokacin da aka samu barkewar cutar a shekarar 2022.
“Rigakafin ba wai tana bayar da kariya dari bisa dari ba ne, amma daga abin da ya faru a lokacin da cutar ta barke a 2022 a nahiyar Turai da nahiyar arewacin Amurka, tsofaffin sun kasance masu karancin hadarin kamuwa da cutar, kuma ana ganin haka ba zai rasa nasaba da kariyar da suke da ita daga rigakafin farankama ba,” in ji farfesa Adam.
Kamfanin hada magungunan rigakafi na Bavarian Nordic ya samar da rigakafin kyandar mpox na MVA-BN sama da miliyan 15, wadda aka tsara bisa tsarin rigakafin farankama - a kasashen duniya 76 lokacin da aka samu barkewar cutar a duniya a shekarar 2022.
4. Korona ta fi mpox saurin rikida
Kwayoyin cutar ‘virus’ na rikidewa a tsawon lokaci sai dai wasu sun fi wasu saurin rikida.
Abin da ya haifar da hakan shi ne saboda sinadaran halitta na DNA ne suke haifar da mpox yayin da sinadarin RNA ne kuma ke haifar da korona.
Masana a Amurka sun ce kwayoyin cuta da suka samu daga sinadaran DNA ba su saurin rikidewa kamar wadanda RNA ya samar.
Akwai nau’uka biyu na cutar mpox - clade 1 da clade 2. Amma kwayar cutar SARS-CoV2 kuwa tana da nau’uka sama da 20.
Barkewar mpox da aka samu a baya-bayan nan ya samo asali ne daga nau’i na farko wanda ale wa lakabi da clade 1b.
“Abin da muke gani a nau’in clad 1b shi ne yana yaduwa ne ta hanyar saduwar aure, amma kuma mun ga yadda yake yaduwa ta hanyar cudanya a gidaje: uwa ta harbi danta da cutar, yara su yada wa juna, ko masu kula da yaron su manna masa,” in ji Trudie Lang, farfesa mai bincike kan lafiya a Jami’ar Oxford.
5. Babu fargabar za a sanya dokar kulle, rufe iyakoki oo wajabta yin rigakafi
Mutane da dama na fargabar ko yaduwar mpox za ta sa a kakaba dokar kulle, abinda zai iya tsayar da duniya cak wuri daya, kamar yadda muka gani a lokacin annobar korona.
Amma duk da cewar cutar ta mpox ta yadu zuwa kasashe 16 na Africa a tsawon shekara biyu da suka gabata, Cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ba ta bayar da shawarar rufe kowace iyaka ba.
“A yanzu haka dai, Cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afirka ba za ta taba bayar da shawarar takaita zirga-zirgar mutane ko kaya ba,” in ji Dr Jean Kaseya.
”Za a ci gaba da zirga-zirga kamar yadda aka saba yi a baya, yayin da mu kuma muke neman abubuwan da za a mu yi amfani da su wajen yaki da yaduwar cita.
Dr Mike Ryan, shugaban sashen daukin gaggawa na WHO shi ma ya amince da hakan.
“Mpox cuta ce da za mu iya magancewa idan mu ka dauki matakan da suka dace a lokacin da ya kamata kuma idan muka hada hannu kamar yadda muka yi a lokacin korona.
Cutar mpox ba ta cika zafi ba kuma da yawan mutane na warkewa cikin mako biyu zuwa hudu. Sai dai wasu cutar na iya yin zafi gare su ta yadda za su bukaci kwantarwa a asibiti.
Mutum zai iya kare kansa daga kamuwa da cutar ta hanyar guje wa cudanya da mutane ko abubuwa ko kuma dabbobin da ke dauke da cutar. Ana bayar da shawarar wanke hannu ko amfani da sanadarin tsaftace hannu bayan taba ciwo ko kuraje.
“Mun san cewa rigakafi kan bayar da kariya, yanzu muna da kayan aiki kuma cutar ba ta da saurin yaduwa sosai,” in ji farfesa Rodney.