Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta kammala cinikin Sterling daga Man City
Chelsea ta tabbatar da kammala daukar dan kwallon Ingila, Raheem Sterling daga Manchester City kan fam miliyan 50.
Sterling, mai shekara 27, ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyar a Stamford Bridge.
Tun da sanyin safiya dan kwallon tawagar Ingila ya yi ban kwana da 'yan wasa da ma'aikatan Etihad ta kafar sada zumunta.
''Na koma Manchester City ina da shekara 20. Yanzu ni cikakken mutun ne,'' in ji Sterling.
''Zan dade ina tuna lashe kofi 11 a kaka bakwai a Etihad har tsawon rayuwata.
City ta dauki Sterling daga Liverpool kan fam miliyan 49 a 2015.
Ya kuma ci wa kungiyar Etihad kwallo 131 a wasa 339 da lashe Premier League hudu.
Sterling wanda ya buga wa Ingila wasa 77, zai zama na farko da Chelsea ta saya abana, tun bayan da attajirai suka sayi kungiyar karkashin jagorancin, Todd Boehly.
Kociyan Chelsea na fatan kara karfin gaban kungiyar, bayan da Romelu Lukaku ya sake komawa Inter Milan, wadda zai yi wa wasannin aro kaka daya.
Dan kwallon Belgium, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Stamford Bridge mai 15 a raga a dukkan fafatawa, sai Kai Havertz mai 14 da Mason Mount mai 13.
Tun bayan da Pep Guardiola ya zama kociyan City a 2016, Sergio Aguero ne kan gaba a cin kwallaye a kungiyar mai 124, sai Sterling da ya ci 120.
Sterling ya zura kwwallo 13 a wasa 30 a gasar Premier League da aka kammala a kakar da ta wuce da daukar lik kuma kofi na 11 jumulla da ya lashe a Etihad.