Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa a Abuja
Yadda aka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa a Abuja
An wallafa
Daruruwan masu zanga-zangar neman saukin matsin rayuwa da ake ciki a Najeriya ne suka fantsama kan titunan birnin tarayyar kasar domin bin umarnin kungiyar kwadago.
Kungiyar kwadago dai ta yi kira da a yi zanga-zangar gargadi ta kwana biyu inda a ranar Talata aka fara gudanar da ita a ranar farko.
Masu zanga-zangar sun kutsa ginin majalisar tarayya domin aikewa da sako ga 'yan majalisar kasar.
Ana sa ran masuzanga-zangar za su ci gaba a rana ta biyu wato ranar Laraba.
Daruruwan al'ummar kasar suka gudanar da zanga-zangar a birane da dama.