Ku San Malamanku tare da Sheik Muhammad Nasir Muhammad

Ku San Malamanku tare da Sheik Muhammad Nasir Muhammad
An wallafa

A wannan karon Ku San Malamanku ya tattauna ne da limamin Masallacin Waje na Kano, wato masallacin da ke Fagge daura da Sabon-Gari, Sheik Muhammad Nasir Muhammad.

A tattaunawarsa da BBC Mallam ya ce an haife shi a birnin Kano, a ranar 13 ga watan Maris na shekarar 1936, wato yanzu yana da kusan shekara 87 ke nan a duniya.

Mallam ya tashi ne a gaban mahaifinsa da kuma kakanninsa na ɓangaren uwa, inda mahaifin nasa ya sanyi shi a makarantar allo har zuwa lokacin da ya sauke Alƙur'ani.

Bayan da ya sauke mahaifin nasa ya ƙara kai shi wata makarantar allon, a gidan su Is'haka Rabiu, wajen Mallam Dantinƙi, inda a can ne kuma ya haddace Alƙur'ani.

A lokacin da aka gina makaranta a Ƙoƙi a 1956, Mallam ya kasance cikin ɗalibanta na farko.

Bayan nan kuma ya tafi makarantar koyon harkokin shari'a ta Kano, inda daga nan, ''sai muka ɗauki jarrabawar Law School, sai aka ce mutum biyar ake soa ɗauka ni ne na shida.''

Ya kara da cewa: ''Ina waccan makaranta ta judiciary ban fi kwana talatin ba sai Premier (Sardauna) Allah ya jikansa sai ya aiko wa principal ɗin makarantarmu Law School, cewa a nemi yaron nan Muhammad Nasir Muhammad a ɗauke shi.''

''To mu kai wannan Law School muka gama, Alhamdulillahi zuwa ɗan wani lokaci kaɗan shi ma ban daɗe da yawa ba sai Mallam Abubakar Gummi sai ya samar min hanyar da zan tafi Madina shekara ɗaya tal sai na dawo.''

Sanadin aminintakarsa da marigayi Ado Bayero

Mallam ya ce a duk duniya ba shi da wani amini da ya fi marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Wannan alaka kuwa ta samo asali ne a dalilin aiki da aka tura Mallam, na mai sa-ido a kan alƙalai, inda aka nemi ya yi rantsuwa kamar yadda ka'idar aikin take amma ya ce shi ba zai rantse ba.

Wannan shi ne farkon alaƙarsa da Ado Bayero, inda ya ce a wannan dalili ne yana zaune agida kawai sai ga direban Sarkin ya zo ya ce, Sarki yana kiransa ya zo gidansa.

''In dai amini ne ba ɗan uwa ba, in dai amini bai kai ya shi ba wallahi, na yarda da shi ya yarda da ni masoyina ne masoyinsa ne ni, babu abin da yake haɗamu ko ya raba mu,'' in ji Mallam.

Yawan iyalin Mallam

Mallam Nasir Muhammad Nasir, wanda ya ce surad da ya fi karantawa a Alƙur'ani ita ce Suratul Yusuf, ya ce yana da 'ya'ya wajen 28 da kuma jikoki wurin 100.