Inter Milan na tattaunawa kan daukar Lukaku da Dybala

Lukaku and Dybala

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata daya bayan komawa Chelsea, Romelu Lukaku ya fada a wata hira da kafar watsa labarai ta Italiya cewar yana son ya sake komawa Inter, hakan ya harzuka magoya bayan Chelsea daga baya ya bara da hakkuri
An wallafa

Babban jami'in Inter Milan, Giuseppe Marotta ya sanar cewar suna kan tattaunawa don daukar dan wasan Chelsea, Romelu Lukaku da na Juventus Paolo Dybala.

BBC ta wallafa cewar Lukaku, wanda ya koma Chelsea kan fam miliyan 97.5 zai amince ya koma Inter koda za a rage masa albashi ne.

Haka kuma jami'in ya sanar cewar suna kan batun daukar dan wasan Roma, Henrikh Mkhitaryan da mai tsaron ragar tawagar Kamaru, Andre Onana daga Ajax.

Lukaku dan wasan tawagar Belgium mai shekara 29, ya ci kwallo 15 a dukkan wasannin da ya yi wa kungiyar Stamford Bridge a kakar da aka kammala har da takwas a karawa 26 a Premier League .

Lukaku, wanda ya bar Chelsea zuwa Everton kan fam miliyan 28 a 2014, ya sake komawa Chelsea daga Inter a matakin wanda ta saya mafi tsada cikin Agustan 2021 kan kwantiragin kaka biyar.

Dan wasan tawagar Argentina, Dybala, mai shekara 28, zai kasance wanda bai da yarjejeniya a karshen watan nan.

Dan wasan Armenia, Mkhitaryan, mai shekara 33, yana cikin 'yan wasan Jose Mourinho da suka lashe sabon kofin Zakarun Turai na Europa Conference League a kakar da aka karkare.

Shi kuwa Onana, mai shekara 26, ya lashe kofi uku na babbar gasar tamaula ta Netherlands, sai dai kuma a bara hukumar kwallon kafar Turai ta dakatar da shi, bayan samunsa da laifin shan abubuwan kara kuzari. Shima kwantiraginsa zai kare.

Inter ta kammala a mataki na biyu a Serie A a kakar da ta karkare da tazarar maki biyu tsakaninta da da AC Milan wadda ta dauki kofin a karon farko tun bayan shekara 11.