Barca ta ci gaba da zama ta uku a La Liga bayan cin Alaves

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Barcelona ta doke Deportivo Alaves 2-1 a wasan mako na 13 a La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

Minti daya da take leda Alaves ta ci kwallo ta hannun Samu, haka suka je hutu ana cin Barcelona kwallo daya.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, Barcelona ta farke ta hannun Robert Lewandowski a minti na 53, sannan ya kara na biyu a minti na 78.

Da wannan matakin Barcelona ta ci gaba da zama a mataki na ukun teburin La Liga da maki 30, ita kuwa Alaves mai maki 12 tana ta 14 a kasan teburi.

Girona ce ta daya a kan teburi da maki 34, sai Real Madrid ta biyu mai maki 32, wadda ta caskara Valencia 5-1 ranar Asabar.

Wasan da Barca da Alaves suka kara a baya:

Sifanish La Liga Lahadi 23 ga watan January 2022

  • Alaves 0 - 1 Barcelona

Sifaniya La Liga Asabar 30 Oktoban 2021

  • Barcelona 1 - 1 Alaves

'Yan wasan Barca da suka kara da Deportivo Alaves

Ter Stegen, João Cancelo, Balde, R. Araujo, I. Martínez, Ferran, Pedri, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña.

Sauran sun hada da João Félix, Christensen, Marcos A., Romeu, Gündoğan, Kounde, Astralaga, Lamine Yamal, M. Casadó da kuma Fermín.