Gane Mini Hanya: Tare da Alhaji Attahiru Ɗalhatu Bafarawa
Tsohon gwabnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Ɗalhatu Bafarawa ya yi jawabi kan matsalar ilimi da tsaro da makomar arewacin Najeriya .
Ya jadada cewa a yanzu dai babu wani ɗan'adawa a fagen siyasar Najeriya da ke adawa domin talaka. Ya ce ƴan siyasar ƙasar su ne ke adawa da kansu da cutar juna game da neman muƙamai ba tare da sun amfana wani abu ba ga talaka.
Bayan yadda yake kallon tafiyar siyasar Najeriya a halin yanzu, tsohon gwabnan ya yi yi ƙarin haske kan wasiƙar da ya aika wa Shugaban Ƙasar Bola Ahmed Tinubu da kuma alƙawarin da shugaban ya yi lokacin zaɓe na samar da wutar lantarki ga talakawan Najeriya.
A tattaunawarsa da Abdou Halilou, ga abin da tsohon gwabnan jihar ta Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ke cewa a cikin hilin mu na GANE MANI HANYA.