Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta yi wasa na 15 a jere ba a doke ta ba a Premier League
Arsenal ta doke Leicester City 2-0 a wasan mako na 25 a Premier League da suka kara a King Power ranar Asabar.
Gunners ta ci ƙwallayen ta hannun Mikel Merino a minti na 81 da kuma saura minti uku a tashi daga wasan.
Shi dai Merino ya shiga karawar a minti na 69, wanda ya canji Raheeem Sterling, bayan da Arsenal ke fama da rashin masu buga gurbin cin ƙwallaye.
Da wannan sakamakon Mikel Arteta ya ja ragamar wasa 15 a jere a Premier League ba tare da rashin nasara ba da cin wasa 10 da canjaras biyar, ƙwazo mai ƙyau tun bayan shekara 14.
Rabon da a doke Gunners a Premier a kakar nan tun 1-0 da Newcastle ta yi nasara a St Jame's Park ranar Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.
Kenan Arsenal ta ci gaba da zama ta biyun teburin Premier League da tazarar maki huɗu tsakani da Liverpool ta ɗaya.
Ranar Lahadi, Liverpool za ta karɓi bakuncin Wolverhampton, kuma da zarar ta yi nasara za ta kara bayar da tazarar maki bakwai.
To sai dai an fitar da Arsenal daga FA da Carabao Cup a bana, kofin da ke gabanta shi ne Premier da take ta biyu a teburi da Champions League da ta kai zagayen gaba kai tsaye.
Arsenal za ta karɓi bakuncin West Ham a Premier League ranar 22 ga watan Fabrairu daga nan ta je Nottingham Forest ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu.