Hojlund na cikin 'yan takarar gwarzon matashi na 2023

An wallafa

Dan wasan Manchester United, Rasmus Hojlund, na cikin 'yan takarar gwarzon matashi na 2023 wato Golden Boy.

Tun farko an bayyana matasan 100 da ke takara, yanzu an rage su zuwa 25 kuma Hojlund yana cikinsu.

Wannan ne karo na 20 da za a karrama matashin dan wasa mai shekara 21 a Turai, bayan da aka kirkiri kyautar a 2003.

Wata jarida ce mai suna Tuttosports ta kirkiri kyautar kuma a lokacin da aka haifi Hojlund.

An fara bayyana 'yan wasa 100 da ke takara a watan Yuni, lokacin dan kasar Denmark yana taka leda a Atlanta, wanda daga baya ya koma Manchester United.

Wasu 'yan wasan United da suka lashe kyautar sun hada da Wayne Rooney a 2004, da Anderson a 2008, da kuma Paul Pogba a 2013.

Anthony Martial ne ya karbi kyautar a 2015 jim kadan bayan ya koma United daga Monaco.

Dan wasan Barcelona Gavi ne ya lashe kyautar ta 2022, wanda a lokacin yana da shekara 19.

Fitattun 'yan jarida ne ke kada kuri'a, inda kowane mutun daya yake da maki 10 a zaben farko, maki bakwai a zabe na biyu, da maki biyar a zabe na uku, da maki uku a zabe na hudu, da maki daya a zabe na biyar.

Ranar 4 ga watan Disamba za a bayyana gwarzon matashin dan wasan tamaula na 2023 a Turin na Italiya, wato Golden Boy.

Jerin 'yan takarar: Jude Bellingham, Jamal Musiala, Xavi Simons, Antonio Silva, Alejandro Balde, Florian Wirtz, Benjamin Sesko, Giorgio Scalvini, Rasmus Hojlund, Levi Colwill, Johan Bakayoko, Milos Kerkez, Arthur Vermeeren, Evan Ferguson, Lucas Gourna-Douath, Warren Zaire-Emery, Ousmane Diomande, Arnau Martinez, Mathys Tel, Andy Diouf, Arda Guler, Bilal El Khannouss, Martin Baturina, Joao Neves da kuma Lamine Yamal.