Idan El-Rufai yana sha'awar NNPP muna maraba da shi - Kwankwaso

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Idan El-Rufai yana sha'awar NNPP muna maraba da shi - Kwankwaso
An wallafa

Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ƙofar jam'iyyar a buɗe take ga duk wanda ke da ra'ayin shiga , ciki har da tsohon gwamnan Kaduna Mallam Nasir El-Rufai.

A baya-bayan nan dai an ga wani bidiyo da ke nuna wata ziyara da Sanata Kwankwason ya kai wa tsohon gwamnan na Kadunan a gidansa.

Mallam Nasir El-Rufai dai ya samu saɓani da gwamnan jihar daya gaje shi, Sanata Uba Sani, abin da ya sa wasu ke ganin zai iya ficewa daga jam'iyyarsa ta APC.