Halin da al'ummar Gwoza ke ciki bayan Amurka ta dakatar da tallafi
Dakatar da tallafin jin ƙai da ake yi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya zai iya bai wa ƙungiyar Boko Haram damar kara samun karfi, a cewar hukumomin agaji.
A watannin baya, rage kuɗin agajin da ake bai wa shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ya tilasta masa dakatar da tallafin da yake bai wa yankin Arewa maso Gabashin ƙasar tallafi.
Kuma a halin yanzu, gaba ɗaya tallafin shirin ya ƙare.
"Dakatar da tallafin da ake bai wa mutane zai saka 'yan Boko Haram su rinjayi matasa su shiga kungiyar, cikin sauƙi wanda hakan zai ƙara haddasa rashin tsaro a ɗaukacin yankin," in ji Trust Mlambo, shugaban ayyuka a yankin daga WFP, yayin zantawa da BBC.
Ƙungiyar Boko Haram ta shahara a duniya bayan da ta sace fiye da dalibai mata 200 daga garin Chibok sama da shekaru goma da suka wuce.



