Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Sasanta Abba Kabir da Sheikh Daurawa da sace ɗalibai a Kaduna
An sace ɗalibai 287 a Kuriga na jihar Kaduna
An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis.
Wani malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi wanda ya kubuta ya bayyana cewa ɗalibai 287 ne aka sace a makarantar.
Sani Abdullahi ya ce "A ɓangaren sakandare ɗalibai 187 ne suka ɓace amma ɓangaren firamare ɗalibai 125 da farko ba a gansu ba amma daga bisani guda 25 sun dawo."
Malamin wanda ya bayyana hakan lokacin da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ziyarci makarantar domin gani da ido yadda lamarin yake , ya kara da cewa "na shigo makaranta misalin karfe 7:45 sai na shiga ofishin principal kuma sai ya ce min in waiga baya, ina juyawa sai naga 'yan bindiga sun kewaye makarantar".
"Mun ruɗe bamu san inda zamu ba, kafin da suka tafi damu daji sai muka canza hanya," in ji Sani Abdullahi.
Malamin makarantar ya ce 'yan bindigar sun kashe mutum daya.
Yaran da lamarin ya rusta da su shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15.
Ya bayyana cewa ana cikin wani hali na fargaba tun bayan sace daliban a safiyar Alhamis.
Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce “Babu wani gida a Kuriga wanda wannan abin bai shafe shi ba”.
Malaman Kano sun sasanta Abba Kabir da Sheikh Daurawa
Gamayyar malaman addinin Musulunci ta jihar Kano ta ce ta sasanta gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da Kwamandan Hisbah na jihar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa bayan rashin jituwar da ta kai ga ajiye aikin shugaban na Hisbah.
Bayan wata ganawa da ta gudana a daren ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar ta Kano, sakataren Gamayyar malaman, Dakta Sa'id Ahmed Dukawa, ya bayyana cewa sun shiga tsakani ne sanadiyyar kiraye-kiraye daga ciki da wajen jihar na ganin an warware matsalar.
A cewarsa, matsayar da aka cimma na nufin cewa a yanzu babu batun murabus din Sheikh Daurawa daga shugabancin Hisbah.
Dukawa ya ce: "Ya (Daurawa) dawo aiki, zai ci gaba da aikinsa".
An shiga ruɗani bayan kisan limami a Zamfara
Al'ummar garin Mada da ke Gusau a jihar Zamfara sun shiga wani hali bayan sun wayi gari da labarin mutuwar limamin masallacin garin, Abubakar Hassan Mada.
Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa an tsinci gawar limanin ne, bayan wasu sanye da kayan sabuwar rundunar tsaron jihar sun tafi da shi a ranar Talata.
Sai dai bayan wani lokaci an tsinci gawar malamin bayan an yi masa yankan rago.
Ɗaya daga cikin mutanen garin na Mada ya shaida wa BBC cewa "Jiya da yamma bayan sallar la'asar wasu sane sa kaya irin na asakarawa suka shigo, an ce mana daga yankin Tsafe suke, sai suka haɗu da askarawa na nan Mada, suka nuna musu gidan liman Abubakar Hassan Mada,"
Ya ƙara da cewa "Bayan da suka fita da shi wajen gari sai suka tsaya suka yi masa yankan rago."
Mutum na biyu da BBC ta zanta da shi wanda shi ma mazaunin garin na Mada ne ya ce: "sun zo sun tafi da shi har suna dariya suna raha, ba mu yi tunanin wani abu ne maras kyau zai faru da shi ba".
Sai dai daga baya gwamnatin jihar ta ce ta kama ƴansintiri guda 10 waɗanda ake zargi da kisan limamin.
Fusatattun mutane sun fasa rumbun abinci tare da yin wawaso a Abuja
Wasu fusatattun matasa sun fasa rumbun adana abinci na gwamnati da ke unguwar Gwagwa a Abuja, babban birnin Najeriya, tare da yin wawason kayan abinci.
Matasan sun yi wa rumbun dirar mikiya ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Lahadi, inda suka yi wawushe buhunan masara da kuma na hatsi.
Mai magana da yawun ƴansandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatarwa da BBC faruwar lamarin, inda ta ce tuni suka tura jami'ansu zuwa yankin domin shawo kan lamarin.
Rahotanni sun bayyana cewa fasa rumbun abincin ya janyo cushewar hanyar Gwagwa-Karmo, wadda kuma ta dangana da anguwan Dei-Dei da kuma wani ɓangare na Jabi.
Ƴan Najeriya da dama dai na ci gaba da kokawa kan matsin rayuwa da suke ciki biyo bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi.
Ba mu da niyyar yin katsalandan a dimokraɗiyyar Najeriya – Janar Lagbaja
Babban hafsan sojin ƙasa a Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja ya jaddada ƙudurin rundunar soji na kare martabar dimokraɗiyyar ƙasar.
Da yake yi wa mahalarta taron ƙarawa juna sani kan aiki da hedikwatar rundunar ya shirya a Abuja, Janar Lagbaja ya ce rundunar ba ta da burin yi wa dimokraɗiyyar ƙasar maƙarƙashiya.
Ya yi kira ga sojojin ƙasar su ci gaba da ba da himma wajen gudanar da ayyukansu.
Alƙawarin da Janar Lagbaja ya ɗauka na zuwa ne sakamakon yunƙurin da aka yi na kifar da gwamnati a yankin Afirka ta yamma da tsakiyar Afirka da suka fuskanci aƙalla juyin mulki bakwai cikin shekara huɗu da ta gabata.
Mali da Guinea da Burkina Faso sai a baya-bayan nan Nijar - dukkansu mambobin ECOWAS sun fice daga ƙungiyar cikin shekaru huɗu da suka gabata.
Chadi da Sudan da ba sa yankin Afirka ta Yamma suma sun fuskanci juyin mulki a 2021.
EFCC ta kama manyan motoci 21 maƙare da kayan abinci
Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin ƙasa ta'annati ta sanar da kama motocin dakon kaya 21 maƙare da kayan abinci da wasu kayayyaki da ke kan hanyar N'djamena a jamhuriyar Chadi da jamhuriyar tsakiyar Afirka da Kamaru.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, an kama manyan motocin ne yayin wani samame da aka ƙaddamar kan titunan Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama a jihar Borno.
Binciken da aka gudanar ya nuna wasu kayan abinci da aka yi dabarar ɓoye su cikin motocin da za su iya wucewa ba tare da an gano ba.
Ƙarin binciken da aka gudanar ya nuna takardar da aka nannaɗe kayan da ke cikin motar ta nuna kayan za a kai su N'djamena a ƙasar Chadi da jamhuriyar Afirka ta tsakiya da kuma Kamaru.