Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta raba maki da Tottenham a Etihad
Manchester City da Tottenham sun tashi 3-3 a wasan mako na 14 a Premier League a Etihad ranar Lahadi.
Tottenham ce ta fara cin kwallo ta hannun kyaftin, Heung-min Son a minti na shida da fara wasa, minti uku tsakani City ta farke, bayan da Son ya ci gida.
Daga nan ne Phil Foden ya kara na biyu, haka suka je hutu City na cin 2-1.
Da suka koma zagaye na biyu Giovani Lo Celso ya farkewa Tottenham, sai dai Jack Grealish ya zura na uku a ragar Tottenham.
Daf da za a tashi wasan kungiyar Ange Posteglou ta farke ta hannun Dejan Kulusevski.
Da wannan sakamakon City ta koma mataki na uku a teburin Premier League da maki 30, Liverpool ce ta biyu mai maki 31, wadda ta doke Fulham 4-3 a Anfield ranar Lahadi.
Tottenham kuwa wadda aka doke wasa uku a jere kafin zuwanta Etihad ta yi kasa zuwa mataki na biyar da maki 27.
Arsenal ce ta daya a kan teburin Premier League da maki 33, bayan wasannin mako na 14.
Ranar Asabar Gunners ta doke Wolverhampton 2-1 a Emirates, hakan ya sa ta ci gaba da jan ragamar babbar gasar tamaula ta Ingila.
Wasannin mako na 15 da za a buga a Premier League:
Ranar Talata 5 ga watan Disamba
- Wolverhampton da Burnley
- Luton Town da Arsenal
Ranar Laraba 6 ga watan Disamba
- Fulham da Nottingham Forest
- Crystal Palace da Bournemouth
- Sheffield United da Liverpool
- Brighton da Brentford
- Aston Villa da Manchester City
- Manchester United da Chelsea
Ranar Alhamis 7 watan Disamba
- Everton da Newcastle United
- Tottenham da West Ham United