Man Utd da Newcastle sun nace wa Sesko, Rodrygo ba ya son barin Madrid

Ɗanwasan gaba na RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Newcastle na shirin sabunta buƙatarta kan ɗanwasan baya na Ingila Marc Guehi inda ta yi sabon tayi na fam miliyan 40, yayin da Crystal Palace ke son fam miliyan 50 kan ɗanwasan mai shekara 25. (Times - subscription required)

Newcastle da Manchester United na hamayya kan ɗanwasan gaba na RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22. (Bild - in German)

Kocin Everton David Moyes na son ƙara shiga kasuwa domin ƙara cefanen ƴanwasa shida da suka ƙunshi ƴanwasan tsakiya guda biyu. (Telegraph - subscription required)

Barcelona ta shaida wa Tottenham cewa sai ta biya fam miliyan 26 kafin ɗauko ɗanwasanta na tsakiya da Spain Marc Casado, mai shekara 21. (Sport - in Spanish)

Ɗanwasan gaba na Brazil Rodrygo, mai shekara 24, na son ci gaba da taka leda a Real Madrid duk da ribibinsa da Tottenham da Arsenal da Liverpool ke yi. (AS - in Spanish)

Crystal Palace na fuskantar hamayya daga Juventus kan ɗanwasan Girona mai shekara 22 Arnau Martinez. (Tuttosport - in Italian)

Ɗanwasan Napoli da Sweden Jens Cajuste, mai shekara 25, na son komawa Ipswich Town maimakon Burnley ko kuma Saudiyya. (Gianlucadimarzio.com - in Italian)

Stuttgart na tattaunawa domin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Portugal Fabio Vieira daga Arsenal. (Athletic - subscription required)