Kayar da APC da PDP ba zai ba mu wahala ba a Jihar Jigawa - Dan takarar ADC

Kayar da APC da PDP ba zai ba mu wahala ba a Jihar Jigawa - Dan takarar ADC
An wallafa

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Dan takarar gwamna a jam'iyyar ADC da ke jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya ya ce kayar da sauran manyan jam'iyyu ba zai masa wahala ba Alhaji Sani Gumel ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.

Alhaji Sani Muhammad Gumel ya ce yana da yaƙinin hakan zai faru duba da irin tsarin jam'iyyarsu wanda tsari ne da matasa suka yarda da shi don ganin a samu sauyi a jihar.