Ra'ayi Riga: Aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron rahoton
Ra'ayi Riga: Aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye
An wallafa

A farkon wannan makon ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye na shekarar 2012 da ya bayar da shawarar haɗe wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati waɗanda ayyukan su ke da alaƙa, a wani mataki na rage kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.

Gwamnatin ta rungumi wannan rahoton ne a ƙoƙarin sauya fasalin wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya duk da cewa hakan zai kunshi rusa wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati da kuma narke masu aiki iri ɗaya da juna a waje guda.

Shin mene ne cikakken bayani kan wannan rahoto?

Kuma ya hakan zai shafi ma'aikata da ma'aikatun da ake magana?

Sannan ya hakan zai taimakawa tattalin arzikin ƙasar?

Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirin ya tattauna a kai.