Modric ya ci ƙwallo mai ƙayatarwa da ta kai Real ta doke Girona

Asalin hoton, Getty Images
Luka Modric ya ci ƙwallo mai ƙayatarwa da Real ta koma ta biyu a teburin La Liga, bayan cin Girona 2-0 a wasan mako na 25 ranar Lahadi.
Hakan ya kawo karshen wasa uku a jere da Real ta kasa cin karawa a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona ce ta ɗaya a kan teburi da maki 54, iri daya da na Real ta biyu da kuma Atletico ta uku da maki 53.
Real ta je ta doke Girona 3-0 cikin Disambar 2024 a gasar ta La liga a wasan farko a bana tsakaninsu, ta ci kwallayen ta hannun Jude Bellingham da Ader Guler da kuma Kylian Mbappe.
Real ta yi wasan ba tare da Jude Bellingham ba, wanda aka dakatar wasa biyu a gasar ta La Liga, saboda jan katin da aka yi masa a karawa da Osasuna.
Alkalin wasan ne ya rubuta a rahotonsa, bayan tashi daga karawar cewar Bellingham ya fada masa kalaman da ba su dace ba.
Kenan ɗan wasan tawagar Ingila ba zai yi wa Real wasan La Liga da za ta fuskanci Real Betis ranar Lahadi ba.
Wasan da ke gaban Real Madrid shi ne ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu da za ta fafata da Real Sociedad a San Sebastian a zagayen daf da karshe a Copa del Rey.
Daga nan Real za ta je Real Betis, domin buga wasan La Liga zagaye na 26 ranar Lahadi 1 ga watan Maris.











