Yaushe ne za a daina ƙarancin dala a Najeriya?
Duk da cewa Babban bankin Najeriya ya yi ta ƙoƙarin shawo kan lamarin tun bayan zuwan gwamnatin shugaba Tinubu amma kullum abin babu sauƙi.
Masana sun ce abin da ke ta’azzara matsalar shi ne ƙarancin dalar a kasuwa da kuma yawan buƙatar ta da ake yi.
Wata matsalar ita ce rashin isasshiyar dalar da za a yi amfani da ita wajen daidaita farashi a kasuwa, sannan kuma babu yarda tsakanin CBN da al’umma.
Yadda darajar naira ta riƙa faɗuwa cikin shekara 10
2014: ₦169:68
2015: ₦196:99
2016: ₦305:22
2017: ₦306:31
2018: ₦306:92
2019: ₦306:95
2020: ₦381:00
2021: ₦410:47
2022: ₦449:05
2023: ₦897:06
2024: (Fabarairu):- ₦1,525
Matakan da za a ɗauka don farfaɗo da darajar naira - Masana
Ya kamata gwamnati ta haɓɓaka babbar hanyarta ta samun dala, wato sayar da ɗanyen man fetur, ta hanyar kara yawan man da take hakowa kai wa kasuwar duniya.
Ya kamata gwamnatin Najeriya ta tabbatar Babban bankin ƙasar ya biya basukan dala da kamfanoni ke bin shi.
Haka nan ya kamata gwamnati ta kara kudin ruwa da aka karba wanda zai sanya masu zuba jari daga kasashen waje su shiga Najeriyar.



