'Abin da ya sa muka cire batun addini a tambayoyin ƙidayar al'umma'
'Abin da ya sa muka cire batun addini a tambayoyin ƙidayar al'umma'
An wallafa
A watan Mayu ne za a gudanar da ƙidayar al'umma a Najeriya, sai dai wani abu da ake ce-ce-ku-ce a kai shi ne cire batun addini a jerin tambayoyin da za a yi wa al'umma.
Nasiru Isa Kwarra, shugaban Hukumar Ƙidaya ta Najeriya ya yi ƙarin bayani kan dalilin hukumar na ɗaukar matakin.