A shirye muke mu zauna lafiya da Rasha - Shugaba Zelensky

A shirye muke mu zauna lafiya da Rasha - Shugaba Zelensky
An wallafa

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya samu tarba ta musamman daga wurin jama'a a yayin da ya ce a shirye kasarsa take ta zauna lafiya, yayin ziyarar da ya kai birnin Kherson, wanda ya sake fadawa hannun kasarsa bayan dakarun Rasha sun janye daga cikinsa.

Tun da farko ya ce masu bincike sun gano cewa an aikata laifukan yaki fiye da 400 a yankin sannan an gano gawarwakin fararen-hula da sojoji.

BBC ba ta iya tabbatar da wadannan zarge-zarge ba, kuma Moscow ta musanta cewa dakarunta sun far wa fararen-hula da gangan.