Yadda tsadar rayuwa ta jefa mutanen Kamaru cikin wani hali
Yadda tsadar rayuwa ta jefa mutanen Kamaru cikin wani hali
An wallafa
Al'umma a Kamaru na fama da matsin rayuwa sakamakon ƙara farashin man fetur karo na biyu a wannan shekarar.
Lamarin ya ƙara jefa mutane cikin matsanancin hali inda mutane ke fama wajen samun abincin da za su kai baka saboda tsadar farashin kayan masarufi.
A wannan bidiyon, BBC ta bibiyi Stella Anchu, wata mazauniyar babban birnin Yaounde don jin yadda take jurewa tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar.



