Abin da ya kamata ku sani game da tasirin cire tallafin mai
Abin da ya kamata ku sani game da tasirin cire tallafin mai
An wallafa
Tallafin man fetur wasu kuɗaɗe ne da gwamnatin tarayya ke cirewa daga cikin aljihunta, waɗanda take amfani da su wurin biyan wani ɓangare na kuɗin da ake kashewa wajen sayowa da shigo da tataccen man fetur daga kasuwannin duniya zuwa Najeriya.
Gwamnatin na yin haka ne domin kada a sayar wa al’ummarta man fetur a kuɗi daidai da ainihin farashin kowace lita, bayan la’akari da ƙudin da aka kashe wajen ɗawainiyar shiga da man daga ƙetare.
A wannan bidiyon, BBC ta yi ƙarin bayani game da tasirin cire tallafin man.




