Kalli yadda hatsabibai ke wasa da babur a 'rijiyar mutuwa'
Kalli yadda hatsabibai ke wasa da babur a 'rijiyar mutuwa'
An wallafa
Wasu hatsabiban mutane a Indiya sun rungumi sana'ar yin kwabo ko kuma wasa da babura a cikin wani rami mai zurfin ƙafa 50.
Ana yi wa ramin laƙabi da "rijiyar mutuwa".
Sun ce suna jin daɗi idan suka ga mutane na nishaɗantuwa da wasan nasu, duk da cewa ba wani kuɗi suke samu masu yawa ba.
"Na sha yanke shawarar daina wannan sana'ar amma idan na tuna tafi da shewar 'yan kallo sai na dawo," a cewar ɗaya daga cikin masu wasan Mohammed Aslam.




