Saka zai iya buga wasan Arsenal da Man city - Arteta

An wallafa

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce Bukayo Saka zai iya kasancewa a cikin 'yan wasan da za su fafata da zakarun gasar Firimiya, Manchester City ranar Lahadi.

Ɗan wasan ya ji rauni a farkon wasan ranar Talata inda Arsenal ta yi rashin nasara da ci 2 - 1 a gasar zakarun Turai da ta buga da Lens.

Saka, mai shekaru 22, ya buga wa Arsenal wasa 87 a jere, inda ya kafa tarihi a kulob din.

Haka kuma an sanya sunan Saka a cikin tawagar Ingila a ranar Alhamis don wasan sada zumunci da Australia da kuma wasan neman gurbin shiga gasar Euro 2024 da Italiya.

Arteta ya ce ya tuntubi kocin Ingila Gareth Southgate game da halin da Saka ke ciki.