Ku San Malamanku tare da Dakta Atiku Shehu Balarabe

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Ku San Malamanku tare da Dakta Atiku Shehu Balarabe
An wallafa

An haifi Dr. Atiku Shehu Balarabe Zawiyya a 1955 cikin Gusau, babban birnin jihar Zamfara a yanzu.

Malamin addinin Musuluncin ya fara karatun allo ko na Islamiyya a Gusau har lokacin da ya yi saukar Alkur'ani, inda ya fada karatun litattafai.

Ya ce ta dalilin wani malami daga kasar Sudan Ustazu Daib Abdurraheem ne, ya samu shiga karatun zamani a Sultan Abubakar College bangaren Higher Muslim Studies, a Sokoto.

Dr. Atiku Zawiyya ya ce tun kafin sannan, Ustaz Daib Abdurraheem ya rika koyar da su darussan Lissafi da Larabci a Zawiyya.

Ya ce a 1977, ya samu damar shiga Jami'ar Bayero Kano, inda ya yi karatun share fagen shiga jami'a, a shekara ta biyu kuma sai ya karkata a bangaren karatunsa a fannin Larabci. Ya sake koma wa Bayero don karatun digiri na biyu.

Cikin malaman da suka yi tasiri a rayuwarsa akwai Sheikh Mallam Murtala Shu'aib da mahaifinsa Mallam Shehu Balarabe da Farfesa Aliyu Na'ibi Suwet da sauran dumbin malamai.

Dr. Atiku Shehu Zawiyya, ya rike mukamai a gwamnatin jihar Zamfara kamar Hukumar Hizba ta jihar, wadda ya sha yi mata shugabanci.