Ba na bacci tun bayan da Atalanta ta ɗura mana 4-0 in ji kocin Juve

Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Juventus, Thiago Motta ya ce yana kasa bacci tun bayan da Atalanta ta ɗura musu 4-0 ranar Lahadi a gasar Serie A, hakan koma baya ne a fatan lashe kofin bana.
An kawo karshen wasa biyar da ba a doke Juventus ba, wadda ta ci gaba da zama ta huɗun teburi da maki 52 da tazarar maki tara tsakani da Inter Milan mai jan ragama.
Tuni dai Juventus ke fuskantar kalubale a kakar nan, bayan da aka fitar da ita a Champions League da kuma Coppa Italia.
''Ya kamata Atalanta ta yi nasara a karawar, mun san yadda suka tsara fuskantar mu,'' kamar yadda Motta ya sanar da manema labarai.
''Sakamakon ya yi muni yana da wahala kafin na yi bacci. Kamar wasan ya juya mana baya, kuma mune Juventus. Magoya baya za su iya na su tunanin.''
Rabon da a doke Juventus da ƙwallo huɗu ko fiye da haka a gida a Serie A tun 1967, sai dai Motta ya ce doke su 4-2 a bugun fenariti a hannun Empoli a Italian Cup zagayen ƙwata fainal shi ne yafi ban haushi.
Ranar Lahadi Juventus za ta fafata da Fiorentina a wasanta na gaba a babbar gasar tamaula ta Italiya.







