Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa ƴan Birtaniya ke rububin buɗe makarantun kwana a Najeriya
- Marubuci, Adaobi Tricia Nwaubani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Letter from Africa series, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Tun shekaru aru-aru, masu hannu da shuni a Najeriya suke sha'awar tura ƴaƴansu makarantun kwana a Birtaniya - amma yanzu nesa ta fara zuwa kusa domin makarantun sun fara rububin buɗe sassansu a Najeriya.
A bara, Charterhouse ta buɗe makarantar firamare a birnin Legas, kuma za ta buɗe sakandare a watan Satumban bana.
Ita ma makarantar Rugby za ta fara sakandare a watan Satumba. Sauran sun haɗa da Millfied da Wellington da Harrow.
Lallai makarantun suna da tsada, amma iyaye ƴan Najeriya masu hannu da shuni suna da tarihin tura ƴaƴansu zuwa Birtaniya domin karatun sakandare.
"Ina farin ciki gaskiya," in ji Karima Oyede, wadda ɗanta yake aji na 10 a Birtaniya, amma zai koma sashen makaranta a Legas a watan Satumba.
Iyaye da dama sun daɗe suna sha'awarar komawa Najeriya, amma suke taraddudi saboda karatun ƴaƴansu.
Duk da cewa akwai makarantun kuɗi masu yawan gaske a Najeriya, samun waɗanda aka wa kallon na duniya ne zai ja hankalin wasu iyayen.
"Ƴan Afirka suna da ra'ayin ba ƴaƴansu ilimi da ke gogayya da na ƙasashen duniya, amma kuma ba su cika son yaran suna rabuwa da al'adunsu ba," Ijay Uwakwe-Okoronkwo, shugaban gidauniyar Nkuzhi Learning Foundation da ke Abuja a Najeriya.
Masanin ilimin, wanda yake ba iyaye da makarantu shawara kan tsare-tsaren ilimi, ya ce wasu ɗabi'un da yaran suke komawa gida da su daga makarantun ne wasu ba sa jin daɗi.
Haka ma akwai fargabar yaɗuwar aƙidar masu auren jinsi, wanda haramtaccen al'amari ne a Najeriya.
"Makarantarmu da tsare-tsaren Birtaniya suke amfani, amma komai namu yana daidai da al'adun Najeriya," in ji John Todd, shugaban Charterhouse a Najeriya.
"Mun san yadda iyaye suke girmama al'adunsu a nan."
Makarantun Birtaniya da suke Najeriya ba su da zaɓi, "dole su bi dokokin Najeriya," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "muna biyayya ga dokoki 100 bisa 100."
Haka kuma makarantar ta ba iyaye dama su ɗauki yaransu a ranakun Lahadi su je coci sai su mayar da su a ranar Litinin da safe.
Akwai abubuwa da dama da suke jan hankalin masu makarantun Birtaniya suke buɗe sassa a Najeriya.
"Najeriya kamar mafari ce domin kutsawa zuwa ƙasashen Afirka, kuma nahiyar Afirka na cikin wadda makarantun ƙasashen waje ke hanƙoro," in ji Mark Brooks.
Mark ya daɗe yana shirya taruka a Najeriya domin tattaunawa a tsakanin makarantun Birtaniya kusan guda 20 da ke ƙasar.
"Babu makarantar da na yi aiki da ita da ba a taɓa samun ɗan Najeriya ya zama shugaban ɗalibai ko mataimakinsa ba.
"Na kawo malamai da dama Najeriya a ƴan shekarun da muke ciki, kuma maganar da ake yi a Birtaniya ita ce mu ƙara riƙe Najeriya da kyau."
Haka kuma tura yara karatu a Birtaniya ya yi tsada. Shekara uku da suka gabata, fam ɗaya naira 500 ne, amma yanzu ya kai 2,200.
Sannan kuma kwanan nan gwamnatin jam'iyyar Labour ta Birtaniya ta ƙaƙaba harajin kashi 20 a makarantun kuɗi.
Bayan kuɗin makaranta, akwai kuma kuɗin jirgi na ɗaliban da ƴan rakiya da masu ziyara.
Don haka buɗe irin waɗannan makarantun a Najeriya sai ya ba iyayen damar ba yaransu karatun da suke so, ba tare da kashe kuɗi sosai ba.
Kuɗin makarantar Charterhouse a Birtaniya ya kusa fam 60,000 (kimanin dala78,000), amma a Legas kuwa, bai wuce fam 15,000.
"Malaman makarantar daga Birtaniya suka zo, amma kashi 90 na masu ƙananan aikace-aikace ƴan ƙasar ne," in ji Mista Todd.
Yawancin iyaye sun fi son yaransu na zuwa makarantun kuɗi, wanda shi ma ya bambanta. Saboda talauci wasu ke tura yaransu makarantun gwamnati, waɗanda yawancinsu kyauta ne, amma ba a koyarwa sosai.
Amma zuwa makarantun Birtaniya ɗin zai zama barazana ga makarantu irin su British International School da ke Legas The Regent School da ke Abuja.
Mista Todd ya yi amannar cewa duk makarantun da za su shiga Najeriya daga Birtaniya za su samu ɗalibai ba tare da sun yi barazana ga waɗanda suke nan ba. Kusan kashi 40 na mutum miliyan 200 ɗin ƙasar ƴan ƙasa da shekara 14 ne.
"Iyaye suna sha'awar makarantunmu sosai," in ji Todd.
"Yanzu haka iyayen da suke zaune a Birtaniya suna turo mana ɗalibai Najeriya."
"Karatu ne za a samu iri ɗaya, amma a farashi mai rahusa. Kuma kusan duk wani ɗan Najeriya yana da ɗanuwa a Legas," in ji shi.
A shekarar 2023, Najeriya ta kasance cikin ƙasashe 10 da aka fi neman bizar karatu, kamar yadda alƙaluman gwamnatin Birtaniya suka nuna.
Amma biyo bayan karyewar darajar naira da tsaurara matakan neman bizar, karatu a turai sai ya ƙara wahala.
A farkon wannan watan, wata ƴarmajalisar Birtaniya, Helen Hayes, wadda ke shugabantar kwamitin ilimi ta ce manyan makarantun ƙasar na fuskantar barazana.
Idan ɗaliban Najeriya suka rage zuwa Birtaniya, jami'o'in ƙasar za su shiga damuwa, inda dole su fara biyo su ƙasarsu domin babu inda za su je su buɗe sassa kamar ƙasar.
Asali ma ai jami'ar farko a Najeriya, Jami'ar Ibadan an buɗe ta ne a matsayin Jami'ar Landan a shekarar 1948.
Ms Uwakwe-Okoronkwo ta ce ƴan Najeriya da dama za su yi farin cikin samun irin wannan damar ta yin karatu a jami'o'in Birtaniya amma a Najeriya saboda za su ƙara mallakar hankali kafin su bar ƙasar.
Adaobi Tricia Nwaubani ɗanjarida ne mai zaman kansa kuma marubuci ɗan Najeriya mazaunin Abuja da Landan.