Ban fitar da ran lashe Premier League na bana ba - Arteta

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mikel Arteta ya ce Arsenal ce za ta lashe kofin Premier League na kakar nan, ba yadda ake hasashen Liverpool ba.

Ranar Laraba Gunners, wadda take da tazarar maki 11 tsakani da Liverpool za ta fafata da Nottingham Forest a wasan mako na 27 a Premier League.

Ranar Lahadi Liverpool ta je ta yi nasara a kan Manchester City da cin 2-0 a Etihad, bayan da Arsenal ta yi rashin nasara 1-0 ranar Asabar a Emirates a hannun West Ham.

Bayan wasan na West Ham Mikel Arteta ya zargi ƴan wasa da rashin sa ƙwazo a fafatawar, bayan da Gunners ta yi kaka 21 rabon ta da kofin Premier League.

Kociyan ɗan kasar Sifaniya ya kara da cewar ''Damar ɗaukar babban kofin tamaula na Ingila na bana ba a hannu na yake ba.''

To sai dai a shirin da Arsenal ke yi na karawa da Forest ranar Laraba, Arteta ya ce ba zai taɓa fitar da ran lashe kofin Premier na kakar nan ba.

Arsenal wadda take sa ran ɗaukar Premier na kakar nan ta ci karo da koma baya, saboda wasu ƴan wasanta da ke jinya.

Kai Havertz da Gabriel Jesus za su ci gaba da jinya har bayan karshen kakar bana, ana sa ran Bukayo Saka zai koma taka leda a cikin watan Maris.

Rabon da Saka ya buga wa Arsenal tamaula tun cikin Disamba, shi kuwa Gabriel Martinelli na ci gaba da jinya.

Kyaftin Odegaard ya yi jinyar da bai buga wasa 12 ba tun farkon fara wasannin bana, an kuma dakatar da wasu ƴan wasan Gunners.

Ƴan wasa biyar na Arsenal aka bai wa jankati a wasa 26 a Premier League kawo yanzu.

Arsernal ta daɗe tana biye da Liverpool a teburin Premier League, tuni Gunners ta kai zagaye na biyu a Champions League, amma an yi waje da ita a FA da Carabao Cup.